1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar rikici a zaben 2015 a Najeriya

November 21, 2014

International Crisia Group na nuna fargaba game da yiwuwar barkewar tashin hankali a 2015 a Najeriya sakamakon neman kakkage madafun iko tsakanin Kudu da Arewa.

https://p.dw.com/p/1DrNg
Hoto: AP

Kungiyar International Crisis Group ta wallafa wani rahoto mai shafi 42 inda ta yi gargadi game da yiwuwar tashe-tashen hankula a zaben shekara mai zuwa a tarayyar Najeriya sakamakon rikici na siyasa da ake fama da shi a kasar. Wannan ya zo ne kwana daya bayan amfani da borko mai sa hawaye da 'yan sanda suka yi a harabar majalisar a lokacin da kakakin ya yi kokarin shiga cikin zauren domin tattauna batun tsawaita dokar ta baci.

Da ma dai rikici siyasa ya zama ruwa dare a lokacin zabe a tarayyar ta Najeriya, inda a zaben 2011 aka sami salwantar rayukan mutane sama da dubu. sai dai kuma Kungiyar ta ce akwai yiwuwar rikici ya kazanta a shekara mai zuwa saboda yakin da bangarorin kudu da kuma arewacin kasar ke yi na neman kakkage madafun iko.

Tuni dai Goodluck Jonathan wanda dan kudu ne ya riga ya bayyana takara a karkashin inuwar jam'iyyar PDP mai mulki. Yayin da babban jam'iyyar adawa ta APC ke shirin fitar da gwani tsakanin 'yan takara da dama galibinsu #'yan arewacin kasar, ciki kuwa har da tsohon shugaban mulkin soja janar Muhammadu Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da kuma gwamnan kano da ke ci yanzu Injiniya Rabiu Musa Kwankaso.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahmane Hassane