1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta kwashe 'yan kasar daga Libiya

July 29, 2014

Rikici na ci gaba da ragargaza kasar libiya shekaru uku bayan kifar da gwamnatin Marigayi Gaddafi

https://p.dw.com/p/1Clqz
Hoto: Reuters

Majiyoyin gwamnatin Faransa sun ce kasar tana shirin kwashe 'yan kasar daga kasar Libiya, sakamakon yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a kasar musamman cikin makonnin da suka gabata tsakanin kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai.

A wani labarin dubban 'yan kasar ta Libiya na tsallaka kan iyaka da Tunisiya domin tsere wa rikice-rikicen da ake samu. Ma'aikatar harkokin cikin gida na Tunisiya ta ce fiye da 'yan Libiya dubu-shida suka shiga kasar a 'yan kwanakin da suka gabata. Wannan ya kawo adadin 'yan kasar kimanin milyan daya da rabi a Tunisiya, galibi wadanda suka shiga domin tserewa rikicin da ya kawar da gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi ta Libiya a shekara ta 2011.

Rahotanni daga garin Benghazi na gabshin Libiya sun ce wani jirgin soji mai saukan ungulu ya fadi lokacin da yake farmaki kan tsageru masu kaifin kishin Islama. Rikicin ya yi sanadiyar hallaka daruruwan mutane, yayin da wasu fiye da 400 suka samu raunika.

Mawallaf: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman