1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fadakar da jama'a game da cutar Ebola

Salissou IssaSeptember 9, 2014

A kasar Guinea gidajen rediyon gwamnati da masu zaman kansu na taka muhimmiyar rawa wajen wayar da ka jama'a game da cutar ta Ebola.

https://p.dw.com/p/1D9SV
Ebola Warnung Symbolbild
Hoto: Reuters

Kasancewar mallakar rediyo abu ne mai sauki ga mafi yawan jama'ar yankunan karkara musamman a kasashen nahiyar Afirka, kuma shi ne aka dogara kai wajen samun labarai. Bisa wannan dalili ne a kasar Guinea, rediyoyin gwamnati da masu zaman kansu suka yunkuro wajen wayar da kan al'umma game da cutar nan ta Ebola da ke ci gaba da salwantar da rayukan jama'a a yankin Afirka ta Yamma.

Lokacin da cutar ta bullu a kasar ta Guinea, rediyoyi masu zaman kansu ne na farko wajen fadakar tare da waye kan al'umma game da wannan cutar da ta kasance bakuwa a yankin. Har yanzu kuwa rediyoyin na ci gaba da nasu kokari wajen sanar da jama'a matakan rigakafi da halin da ake ciki kan cutar ta Ebola mai saurin kisa. Umaru Kamara dan jarida ne a tashar Radiyo Liberte FM da ke Konakry babban birnin kasar, ya yi karin haske.

"Muna maganar Ebola a cikin labaranmu, muna bayyana wa masu sauraro ci gaban cutar da yankunan da ta fi kamari, hadda sabbin mutanen da suka kamu cikin mako. Sannan mun kirkiro da shirye-shirye da masu sauraro ke kira don yin tambayoyi a kan cutar don dai su gane da kyau cikin harsunanmu na gida."

Kira ta waya kai tsaye don neman bayani

Kind mit Ebola in Kailahun Sierra Leone 15.08.2014
Hoto: Carl De Souza/AFP/Getty Images

Yayin shirye-shiryen gidajen rediyon, masu sauraro na yin waya kai tsaye da yin tambayoyi dabam-dabam, abinda ya sa tilas ma'aikatan rediyo na gwamnati da masu zaman kansu ke yin baki daya don bada labarai iri daya kan cutar, don kada a rikita al'umma kamar yadda Umaru Kamara ke cewa.

"Akwai masu sauraron da ke da ra'ayin cewa babu ma cutar ta Ebola. Aikinmu shi ne nuna masu cewa tabbas akwai wannan cuta a nan Guinea da ma wasu kasashen Afirka ta Yamma. Wasu kuma sun yarda akwai cutar, amma suna tambayarmu yaya ake kare kai. Dole muke basu amsa ta hanyar hujjoji. Gaba ki daya rediyoyi a nan Guinea amsa daya muke bai wa masu sauraro dangance da cutar ta Ebola. Kaga in hukumomin lafiya suka ce mutum daya ya kamu, mu rediyoyi muka ce ukku ne, zai tada hankulan jama'a, shi ya sa muke baki daya."

Karancin wayarwa da jama'a kai a wasu kasashe

Guinea Ebola Aufklärung Gesundheit Hygiene
Hoto: Reuters/Unicef

Sai dai yayin da a kasar Guinea gwamnati ke aiki da rediyoyin don wayar da kan al'umma, a Jamhuriyar Nijar saniyar ware aka maida rediyoyin musamman masu zaman kansu. A Nijar din akwai nakasu game da sakonni na waye kai da magabata da likitoci suke watsawa ta kafafen yada labaru game da cutar. Duk da cewa kasar ta hada iyakar kilomita 1,500 da Tarayyar Najeriya inda wasu suka kamu da cutar. Ali Abdou shi ne daraktan Radiyo Garkuwa a birnin Maradi ya koka yana mai cewa.

"Ba abin da hukumomi suka yi na waye kan jama'a game da Ebola. Har yanzu shuru kake ji daga hukumomi da masu aikin kiwon lafiya da hukumomi na jiha. Mun je mun ga gwamnan jiha a kan jawo hankalin mutane bisa matakan da ya kamata a dauka na rigakafi, ganin Maradi na da iyaka da Najeriya kuma akwai hada-hada ta shige da fice sosai tsakanin kasashen biyu. Amma sai suka ce ba sa son a tayar da hankalin mutane. Ka gani idan wadanda ya kamata su yi bayanin ba su yi ba, to mu me za mu gaya wa mutane."

A kasar Guinea kasancewar wasu yankunan na da wahalar zuwa, magabatan na amfani da gidajen rediyon karkara don aika sakonni kan cutar ta Ebola da matakan kare kai zuwa ga jama'a.