Ebola: Tsoron barazanar yaɗuwarta a duniya
Sama da mutane 4,400 suka mutu daga Cutar Ebola. A karon farko dai an samu mutuwar mutane biyu daga Turai da kuma Amirka, batu da ke barazanar yiwuwar ɓarkewar cutar a duniya baki ɗaya.
Dallas-Amirka
A Dallas, Texas, ma'aikatan kiwon lafiya guda biyu sun kamu da ƙwayoyin Cutar Ebola a lokacin da suke kula da lafiyar Thomas Duncan, wanda ya je Amirkan daga Laberiya, daga ƙarshe kuma ya mutu. A birnin Madrid ɗin Spain ne dai aka samu ɓullar cutar a karon farko a wajen Afirka ta yamma, inda wani jami'in kula da lafiya mutu bayan kamu da ƙwayar cutar ta Ebola.
Meliandou- Guinea
A ƙauyen Meliandou da ke ƙasar Gunea ne dai aka fara samun ɓullar Cutar Ebola a bara. Inda wata yarinya mai shekaru 2 da haihuwa da ta fara kamuwa da cutar ta mutu a watan Disamba. Daga bisani 'yar uwarta da mahaifiyarta da kakarta suma suka mutu sakamakon kamuwa da cutar. a watan Maris na 2014 ne ma'aikatar kiwon lafiya ta Guinea ta sanarwa Hukumar kula da Lafiya ta Duniya WHO, ɓullar Ebola.
Monrovia- Laberiya
A yanzu haka Ebola na yuɗuwa kamar wutar jeji a wasu sassan Sierra Leone, Guinea and Laberiya. A Monrovia babban birnin Laberiya, yajin aikin ma'aikatan kiwon lafiya ya ƙara kazanta lamarin. Sai dai a ƙasashen Najeriya da Senegal an cimma shawo kan matsalar yaɗuwar cutar.
Geneva-Switzerland
Ebola na yaɗuwa ne ta ruwan jikin mutun, musamman jini da amai da wasu abubuwa masu nasaba da ɗiwa. Dangane da haka ne jami'an jinya ke fuskantar hatsarin kamuwa da ita. Ƙwararrun a fannin kiwon lafiya a Geneva, sun jaddada amafani kayan rufe jiki da na kariya. A duniya baki Ɗaya dai jami'an kiwon lafiya sama da 400 suka kamu da kwayoyin cutar.
Manila- Philippines
Bincike ya tabbatar da cewar wajen mutane 4,000 ne suka kamu da Cutar Ebola. Sai dai WHO ta ƙiyasta cewar akwai ninkin hakan da ke Fama da cutar. A wani taron da aka gudanar a Manila a ranar Litinin, shugabar hukumar ta WHO, Margaret Chan, ta ce duniya gaba ɗaya na cikin barazana. In Asiya,alal misali har yanzu mutane ba sa kamuwa da Ebola.
Frankfurt da Leipzig- Germany
A Jamus, wani mutum da ya kamu da Ebola a yankin Yammacin Afirka kuma aka kai shi Leipzig ya mutu a asibitin St. Georg a ranar 14 ga watan Oktoba. A yayin da ake jinyar wani mutum guda a birnin Frankfurt. Ministan lafiya Hermann Gröhe ya nunar da cewar babu barazanar yaɗuwar cutar a Jamus.