1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola ta kashe mutane 31 a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango

September 2, 2014

Da farko Jami'an lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango sun bayyana cewa mutane 13 ne kawai suka mutu ta sanadiyar wannan cuta ta Ebola.

https://p.dw.com/p/1D5If
Plakat mit Ebola-Warnung
Hoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da ofishin MDD sun bayyana cewa, bayyanar annobar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango ta kashe mutane 31, duk kuwa da cewa bazuwar cutar ta takaita ne a yankin arewa maso yammacin kasar.

Eugene Kambambi, wanda ke magana da yawun Hukumar ta WHO a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango, ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mahukuntan wannan kasa sun yi kokari wajen ganin sun takaita bazuwar cutar da tazarar kimanin kilomita 800 arewa daga birnin Kinsasha fadar gwamnatin kasar.

Jami'an lafiya tun da fari sun bayyana cewa mutane 13 ne kawai suka mutu ta sanadiyar wannan cuta, Kambambi wanda ke tare da ministan lafiya na Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango Felix Kabange Numbi ya bayyana cewa ya zuwa yanzu akwai mutane 53 da aka tabbatar da ganin cewa sun harbu da kwayoyin cutar ta Ebola, sannan akwai karin wasu mutanen 185 da ake duba lafiyar su saboda dalilan mu'ammalarsu da mutanen da aka tabbatar sun harbu da kwayoyin cutar.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu