Amsoshin takardunku
Tarihin Jean Bedel Bokassa
Tarihin tsofan shugaban ƙasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mirganyi Jean Bedel Bokassa
Jean Bedel Bokassa tsofan shugaban ƙasar Afirka ta Tsakiya
A yaushe ne shugaba Jean Bedel Bokassa yayi mulkin
ƙasar Afrika ta tsakiya ? ta ƙaƙa ya zo mulki kuma ƙaƙa
ya sauka daga kujera mulkin ?
Tarihin Jean Bedel Bokassa na da matuƙar tsawo saidai a
taƙaice an haife shi ranar 22 ga watan Febuaru nan shekara
ta 1921 a wani ƙauye mai suna Bobangui.Kuma asulin
iyayensa ´yan cirani ne, da suka zo daga ƙasar Cote
d´Ivoire.Tun yana ɗan shekaru shida ya zama maraye, bayan
da turawan mulkin mallakar ƙasar Faransa suka bindige
ma´aifinsa.
im kaɗan bayan haka itama ma´aifiyarsa ta kashe kanta.
To amma kasancewar sa maraya ba uwa ba uba, ta ƙaƙa
yayi karatu ya shiga siyasa har ya kai ga matsayin
shugaban ƙasa ?
Hausawa kan cewa wai ƙaddara ta riga fata.
To bayan rasuwar iyayensa sai dangi sa suka karɓe shi suka
tatala.Kuma sai ya kasance a makaranta yaro mai ƙwazo da
basira, saboda haka ma sai maluman sa a lokacin turawan
mulkin mallaka suka bukaci ya zama wani limamin krista, to
amma sai ya fi nuna shawar shiga aikin soja.Ta haka ne ya
shiga rundunar sojojin ƙasar Faransa a shekara 1939.Yayi
yakin Indochine da Algeriya.
A game da batun siyasa kuwa ya shigi gadan gadan a
shekara 1064 bayan da ɗan uwansa, shugaban ƙasar Afrika ta
tsakiya na farko cewa da David Dacko ya naɗa shi shugaban
rundunar sojoji ta ƙasa.
Bayan an yi shekara guda sai wani daga cikin manyan sojojin
ƙasar yayi yinƙurin hamɓar shugaban ƙasa, ya kuma buƙaci
cafke Bokassa, to saidai Allah bai bashi sa´a ba.Jean Bedel
Bokassa yayi nasara murƙushe wannan yinƙurin juyin mulki,
to amma a wani mataki na kogo ya juye da mujiya, sai yayi
amfani da wannan dama, domin kifar da shugaban ƙasa
David Dacko, to kaji yadda Bokassa ya hau karagar mulki a
Afrika ta Tsakiya ranar 31 ga watan Disemba na shekara ta
1965.
To bayan ya hau mulki ƙaƙa ya gudanar da harakokin
jagorancin ƙasar ?
Jim kadan bayan hawansa karagar mulki ya kawo cenje -cenje
da dama, wanda kuma jama´a suka yi marhabin da su,
mussamman ta ɓangaren noma da mallakar filayen noma da
kuma yaki da cin hanci da rashawa.Duk da kama karya da ya
shimfiɗa, yayi matuƙar farin jini ga jama´a a shekaru bakwai
na farko, kuma mulkin nasa ya samu babban goyan baya
daga ƙasar Faransa.
To saidai tarmamuwar Bokassa ta fara dushewa tunranar biyu
ga watan Maris na shekara ta 1975 inda ya aiyanar da kansa
amatsayin shugaban ƙasa har sai ƙarshen rayuwarsa.Shekaru
biyu bayan haka ya naɗa kansa Marshal.
Sannan ya naɗa kansa sarkin sarakuna a watan Disemba na
shekara ta 1977.
Shin da gaske ne Jean Bedel Bokassa ya musulunta ?
Ƙwarai kuwa wannan magana gaskiya ce.Jean Bedel Bokassa
ya musulunta a shekara 1976 inda ya cenza suna zuwa Salah
Eddine Ahmed Bokassa.A cewar rahotanin daga ƙasar,
shugaban ƙasar Libiya ne Muhamar Ƙaddafi ya musuluntar da
shi.
Ta la´akari da kyakkawar karɓuwar da ya samu daga
jama´a amma ta ƙaƙa kuma mulkin ya kufce masa ?
Sanadiyar baƙin jinin Jean Bedel Bokassa ta samo asuli daga
cenje cenje barkatai da yayi ta aikatawa da kuma mulkin
kama karya da ya ƙaddamar.Misali a shekara 1979 ya umurci
jami´an tsaro su fattataki ´yan makaranta a lokacin wata
zanga zanga, sannan an zarge da da hannu acikin kissan
wasu ɗallibai 100 bayansu shirya zanga zangar nuna adawa
da sanya kaya iri ɗaya a cikin makaranta.Sai kuma tuhumar
sa da ake yi da leffin maita.
A cikin wannan yanayi ne na taɓarɓarewar al´amura cikin a
daren 120 ga watan Satumber na shekara ta 1979 a yayin da
Bokassa ke ƙasar Libiya, jami´an leƙen asiri tare da hadin
gwiwar ƙasar Faransa suka kadamar da wani hari da suka yi
masa juyin mulki.Kuma shugaban ƙasar da ya hamɓare wato
David Dacko shine ya sha fansa,kuma ya koma kan kujerarsa.
Shikuwa Jean Bedel Bokassa ya shiga gudun hijira ƙasar Cote
d´Ivoire sannan ya tafi Faransa.Ya koma Jamhuriyar Afrika ta
Tsakiya a shekara 1986 duk da cewar kotu ta yanke masa
hukuncin kisa.Shigar sa ke da wuya kotu ta sa aka cafke shi
an ka sake yi masa shari´a aka sake jaddada hukuncin
kissan.Saidai kuma shekara ɗaya gabani, kotu ta sassauto
hukuncin zuwa ɗaurin rai da rai, sannan ya koma ɗaurin
shekaru goma.Shugaban ƙasa Andre Kolingba yayi masa
afuwa gaba ɗaya a shekara 1993.
Jean Bedel Bokassa ya mutu sanadiyar ciwon bugun zuciya a
shekara 1996.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Abdulahi Tanko Bala