1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duniyar ɗan Adam

Aikin taimakon jin ƙai a ƙasar Haiti

Hukumomi da ƙungiyoyin agaji na bada gagarumar gudunmawa wajen aikin jin ƙai a Haiti.

Aikin taimakon jin ƙai a Haiti

Gajeren saƙo na SMS dake faɗakarwa game da aukuwar girgizar ƙasar shine abinda ya fara jan hankali wajen shirya gagarumin aikin ceto mafi girma a tarihin hukumar taimakon agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya. Saá guda da aukuwar girgizar ƙasar ne cibiyar tattara bayanai da akewa da saƙonni ta Majalisar Dinkin Duniya game da aukuwar balaoí daga indallahi ta riƙa aikewa da saƙonni tare da yin gangamin dubban maaikatan agaji a faɗin duniya domin taimakawa. Nan da nan hukumomi da ƙungiyoyin agaji masu zaman kansu tare da jamián aikin jin ƙai na sa kai da likitoci suka fara baiyana aniyarsu ta kai ɗauki domin aikin ceto. Thomas Peters jamií ne a ofishin hukumar tsara ayyukan  bada agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya dake Geneva.

"Ba tare da wata wata ba muka ankarar da jamián mu. Hasali ma dai a cikin saoi shida muna iya haɗa kan dukkanin jamiái domin irin wannan aikin ceto na gaggawa inda suka farawa da tantance girman taádi da kuma yawan mutanen da ake zato lamarin ya rutsa da su. Muna kuma dubawa a irin wannan yanayi ko akwai jamián Majalisar Ɗinkin Duniya da suka rasa rayukan su. Wannan shine matakin farko kuma mafi muhimmanci, sanin ko akwai abokan aikin mu da balaín ya rutsa da su".

Tawagar dake wannan aikin bincike da tattara bayanai ta haɗa da ƙwararun jamian bada agajin gaggawa waɗanda suka sami horo na aikin ko ta kwana. Za kuma a iya kiransu a kowane lokaci idan wata annoba ta faru a cewar jamiár ƙungiyar tsara ayyukan taimakon agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya dake birnin Geneva Elisabeth Byrs.

Jamian tsaron Majalisar Dinkin Duniya ke taimakawa wajen taimakon jin ƙai.

" Akwai ƙwararu ta fannin tsaron lafiyar jamaá da jamián kiwon lafiya da masana harkar samar da ruwan sha dana yanayin ƙasa. Mutane dai daga dukkan fannoni na rayuwa kuma ɗan abinda ake biyansu a matsayin albashi bai taka kara ya karya ba. Waɗannan rukuni na mutane sune na farko da ake turawa a yayin da aka sami aukuwar balaí daga Indallahi, kamar Ambaliyar tuwa, girgizar ƙasa ko kuma ɓarkewar annobar cuta. Su kan yi nazarin halin da ake ciki sannan su sanar da ƙungiyoyin ayyukan taimakon jin ƙai game da irin abin da aka fi buƙata. Sune kuma har ila yau suke tsara aikin cibiyar taimakon jin ƙan wanda kamar yadda aka sani yake cigaba yanzu haka a ƙasar Haiti".

Yayin da ofishin hukumar tsara ayyukan taimakon agajin ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da halin da ake ciki da kuma irin taimakon da ake buƙata a Haiti ya sanya hukumomin gaji daga sassan duniya suka yi ta tururuwa zuwa Port-au-Prince babban birnin Haiti domin taimakawa alúmomin yankin dake zaune akan tsaunuka game da raunukan da suka samu tare da basu magani da kulawar gaggawa. Ƙasashen masu bada agaji sun buɗe shafi na yanar gizo domin sanar da masu buƙatar bada taimako, hukumomin da zasu tuntuɓa.

Ko da yake da farko baá tantance girmar taádin da girgizar ƙasar ta yi a Haiti ba, a cewar Thomas Peter hanzarin da aka yi na tura jamián agaji cigaggawa ya taimaka matuƙa, domin bai kamata dama a bata lokaci ba.

" Ba buƙatar ɗaukar lokaci mai tsawo Idan muhimmin abu irin wannan ya faru ba wanda ke buƙatar agajin gaggawa, ka yi kira ga jamaá su fito domin taimakawa. Tun daga filin jirgin sama akan iya sauya tsarin taimakon idan ya kasance girman abinda ya faru bai kai yadda aka yi tsammani ba, ko kuma idan inda aka kai taimakon suka ce basa buƙatarsa. Akan sami irin wannan yanayi misali wajen kai ɗaukin gobara, inda akan tura motocin kashe gobara da yawa idan kuma ba buƙatarsu suna iya dawowa.

Akwai dai daraussa da dama da Majalisar Ɗinkin Duniya ta koya daga kurakurai na baya na ayyukan taimakon agaji da suka faru a wurare da dama. ƙalubalen da aka fuskanta shekaru goma da suka wuce na aikin ceto a mawuyacin yanayi sun sanya a wancan lokaci aka riƙa kai kayayyakin da basu ake buƙata ko kuma a wasu lokutan taimakon agajin kan isa a makare, a saboda haka ne ya sa yin kyakyawar tsari gabanin kai taimakon agaji yake da matuƙar muhimmanci. A yanzu an tsara sabon fasali inda farko ake nazari tare da tantance ainihin taimakon da ake buƙata na agaji sannan a fayyace waɗanda suke sune muhimman buƙatu a kuma tsara yadda zaá aiwatar da aikin taimakon jin ƙan tare da haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin agaji da kuma gwamnatin ƙasar da aukuwar wannan balaí ko annoba.

Daya daga cikin titunan Port au Prince a ƙasar haiti

A kowane lokaci ana ɗaukar bayanai na haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya kamar a ɓangaren lafiya da rabon abinci da sufuri hakazalika da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu waɗanda ke cikin aikin taimakon jin ƙan.

Shigar da ƙungiyoyi masu zaman kansu a gagarumin aikin bada agaji irin wanda ke gudana a ƙasar Haiti ƙarƙashin inuwar Majalisar Ɗinkin Duniya abu ne mai kyau domin tafiyar da komai cikin tsari sai dai kuma alámuran basa tafiya yadda ake buƙata a cewar Thomas Peter

"Yawancin ƙungiyoyi ne na taimakon alúma wanɗanda ke da niyar sadaukar da kansu domin aikin alheri, kuma babu shakka ban ga abinda zai sa ba zasu aiki na gari ba. To amma yadda zaá amfana da basirar su na buƙatar shigar da su cikin tsarin aikin bayar da agajin ƙarƙashin kulawar Majalisar Ɗinkin Duniya. Sai dai ya kamata a fahimta matsalolin da aka samu a filin jirgin saman Haiti wanda wani yanki nasa ya lalace, bashi da sarari mai yawa da zai iya ɗaukar jirage da dama da kuma sauke kayayyakin da suke ɗauke dasu. A saboda haka tsara tashi da saukar jiragen dake kawo agaji na ɗaukar lokaci, wannan ya sa wasu jiragen dole su juya ba tare da sun sauke kayan da suka kawo ba. Wannan lamari ya sanya damuwa da ɓacin rai matuƙa".

Ƙananan yara da suka zama marayu sakamakon rasuwar iyayensu a girgizar kasa.

Sojojin Amirka su ke riƙe da ragamar  gudanarwar filin saukar jiragen saman na Port-au-Prince da kuma aiwatar da tsarin jigilar jiragen dake kawo agajin. Maáikatan agaji dai sun yi maraba da wannan mataki sai kuma wasu ƙungiyoyin agajin sun koka da cewa Amirkawan sun fi bada fifiko ga kayan agajin da aka kawo daga ƙasar Amirka yayin da wasu muhimman kayayyakin buƙatu da aka kawo daga sauran wurare suke jibge.

Wannan abu a bayyane yake ba ma kawai a sararin samaniyar Port-au-Prince ba, harma da wuraren ajiyar kayayyaki a filin jirgin. Idan aka sauke kaya, sai an bincika a adana sannan a sake karkasa shi wajen rabawa. A saboda haka ƙungiyoyin agajin ke buƙatar haɗa hannu da wasu ƙungiyoyi na cikin gida a Haiti domin raba kayayyakin ga jamaá. Abu na farko dai akwai samun manyan motoci da zasu dau kayayyakin sannan da man da motocin zasu sha bugu da ƙari kuma da jamián tsaro da zasu yiwa motocin rakiya. Ƙalubalen dai yana da yawa.

Elisabeth Byrs mai magana da yawun ƙungiyar tsara ayyukan taimakon agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya dake birnin Geneva tace suna jin ƙorafe-ƙorafen da ake yi a Haiti cewa taimakon agajin na zuwa a makare kuma baá yi cikakken tsari ba. Tace akwai buƙatar yin uzuri ga jamián dake gudanar da aikin agajin tare da sauran ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa waɗanda ke aiki ba dare ba rana don taimakawa alúma.

" Waɗanda ke ƙorafin cewa aikin taimakon agajin na tafiyar Hawainiya ko kuma Majalisar Ɗinkin Duniya bata yin azama, to ina sanar da  su cewa wannan aiki ba abu ne da zaka ɗora a Sikeli ba, domin girman wannan balaín girgizar ƙasa da taádin da ta yi ya fi gaban kace ka wayi gari a rana guda ka wadatar da kowa da kowa. ba zai yiwu ba". 

 

 

Ƙari daga wannan rukuni