1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duniyar ɗan Adam

Taimakon Majalisa Ɗinkin Duniya ga Haiti

Ƙasashen Duniya ke ci gaba da kai gudumawar magunguna da abinci zuwa ƙasar Haiti da bala'in gigizan ƙasa ya aukawa.

Halin rashin sanin tabbas a Haiti bayan girgizar ƙasa

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi alƙawarin ƙaddamar da Asusun taimakon raya ƙasa na Dalar Amirka miliyan 560 da nufin samar da magunguna da matsagunan zama da kuma abinci ga al'umar ta Haiti dake neman taimakon gaggawa.

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban ki-Moon ya bayyana aniyar sa ta isa ƙasar ta Haiti domin duba irin ɓarnar da girgizar ƙasa ta yi wa al'umar Haiti, tare kuma da shirya yadda za'a ci gaba da taimakawa ƙasar domin farfaɗowa daga cikin wannan bala'i da ta samu kanta a ciki.

Kamar yadda MƊD ta yi bayani za'a ƙaddamar da asusun Dala miliyan 560 ne domin samar da ruwan sha da matsugunai da sauran buƙatun yau da kullum da al'umar ta Haiti ke nema domin rage raɗaɗin wannan bala'i kamar dai yadda babban magatakardan MƊD yayi ƙarin haske.

Ban Ki Moon yace "MƊD zata ƙaddamar da asusun gaggawa na Dala miliyan 550. Akasarin kuɗin za'a yi anfani da su ne wajen samar da buƙatun gaggawa. Irin su ruwan sha da abinci da yanzu haka ake ƙarancin su. Idan aka yi la'akari da yawan mutane dake kwana a filin Allah ta'ala ba tare da gidaje ba, dole ne mu samar masu da matsugunai. Muna buƙatar tantuna masu yawan gaske"

Yanzu haka dai wani ƙiyasi da MƊD ta fitar ya nuna cewa tuni wasu ƙasashe kimanin ashirin da kanfanoni daban-daban suka yi alƙawarin samar da dala miliyan 268.5 ga al'umar wannan ƙasa da yanzu aka ƙiyasta cewar mutane kusan dubu 200 suka rasu sakamakon wannan girgizan ƙasar da yanzu haka aka ce ya shafi aƙalla mutanen ƙasar miliyan uku.

Koda yake a ta bakin Ban Ki-Moon har yanzu wannan adadi ne da ake ƙiyastawa. Yace "har yanzu babu wanda zai ce ga yawan mutane da suka halaka ko suka samu raunuka, abinda ake bayyanawa bai wuce shaci faɗi ba. Yanzu dai kowa yana ganin abinda ya faru da idanun sa, don haka ba sai na ƙara cewa komai ba akai. Ina dai sauraren cikakken bayanai daga ofishin mu dake. Kuma da zarar mun samu zamu sanar da ku".

Tun bayan da wannan girgizar ƙasar ta auku ne dai ƙasashen duniya manya da ƙanana suka tashi haiƙan wajen ba da gudumawar gaggawa ga al'umar ta Haiti, inda Amirka da sauran ƙasashe irin su Brazil da Birtaniya da Jamus da China suka aike da jami'an kiwon lafiya da kuma tan-tan na abincin gwangwani da ruwan sha domin tallafawa al'umar ta Haiti.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Mohammad Nasiru Awal

Ƙari daga wannan rukuni