1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duniyar ɗan Adam

Taron Kopenhagen da matsalolin sauyin yanayi

Duk fatan da aka yi na cimma wata yarjejeniya mai gamsarwa a taron sauyin yanayi da aka kammala a ƙarshen mako a birnin Kopenhagen, ya ci-tura.

Masu zanga-zanga a ranar ƙarshe na taron Kopenhagen

Maimakon yarjejeniyar, alƙawari aka ɗauka don a samu sukunin tattaunawa kan batun yanayin a cikin watanni masu zuwa. To sai dai a daidai wurin da ´yan siyasa suka gaza, ƙungiyoyin farar hula na ƙasa da ƙasa ne suka nuna bajimta.

Taron ƙolin kan sauyin yanayi yayi kama da wani bikin ɗaurin aure wanda ya sauya zuwa wata jana´iza. Duk ƙasashen duniya sun hallara a birnin Kopenhagen da zumar cimma wata sabuwar yarjejeniya don shawo kan matsalar sauyin yanayi tare da ɗora duniya kan sabuwar turba ta samun yanayi kyakkawa. A taron manema labarai bayan taron an jiyo shugaban Amirka Barak Obama yana mai cewa.

"Abin da muka cimma a Kopenhagen ba shi ne ƙarshe ba, a´a mabuɗi ne na wani sabon zamani ne na ɗaukar mataki na ƙasa da ƙasa."

Shugaban na Amirka ya haƙiƙance cewa da shi da sauran takwarorinsa na ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki za su yi ƙoƙari don su albarkaci matsayin da aka cimma a tattaunawar. To amma hakan ya ci-tura domin an kasa cimma wata yarjejeniya duniya dangane da sauyin yanayi. Shugaban Green Peace Kumi Naidoo ya ce hakan shi ne mafi a´ala.

"Ba zamu yarda wani gungun wasu ƙasashe komin ƙarfinsu su yiwa shirin Majalisar Ɗinkin Duniya yankan baya ba. Da hakan na nufin an yi fatali da aƙidar nan cewa duk ƙasashen duniya ɗaya suke kuma ana sauraran kokensu gaba ɗaya, saboda wai wasu ƙasashe biyar ko shida za su faɗawa sauran duniya abin da za ta yi."

Ganin cewa tawagogin ƙasashe da yawa musamman daga yankin Latun Amirka na da wannan ra´ayi ya sa an yi fatali da yarjejeniyar. A ƙarshe an fid da wata takarda ce wadda mai so zai sanya mata hannu wanda bai so kuma ya yi watsi da ita.

Mai yiwuwa kuma tawagogi kimanin 192 da suka hallara a Kopenhagen sun haɗu da sabbin ƙawaye da ba su zata ba. Saɓanin gwamnatoci ana iya cewa ƙungiyoyin farar hula na duniya sun tsallake siraɗi dangane da shirin haɗakar duniya bai ɗaya, domin sun dage kan manufarsu musamman bisa shawarwarin masana kimiyya. Ba a ga wani banbanci tsakanin talaka da mai kuɗi ba, kana kuma sun nuna a filin cewa ba kawai cikakkiyar masaniya kuma shirye suka shiga zauren taron ba, sun kuma dage kan matsayinsu yadda ya kamata. A gun taron manema labarai na farko bayan da shugabannin ƙasashe suka yi saurin ficewa daga birnin na Kopenhagen, shugaban asusun kare namun dawa na dunia Kim Carstensen cewa yayi.

"Rashin kyaun wannan yarjejeniya na da wata fa´ida, domin ba a tilastawa kowa amincewa da ita, kuma kowace ƙasa ka iya sanya na ta burin. Ba ta hana mu ɗorawa ƙasashe nauyin ɗaukar ƙarin matakai bisa manufa ba a ci-gaba da wannan shiri na neman mafita daga sauyin yanayi."

Ko da yake za´a ci-gaba da tattaunawa kan batun sauyin yanayin to amma zai fi kyautuwa matakan da za su biyo a aikace su fito daga ƙasa amma ba sama ba.

Mawallafa: Helle Jeppesen/Mohammad Nasiru Awa

Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Ƙari daga wannan rukuni