1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duniyar ɗan Adam

Shekaru 25 da haɗarin Bhopal

Mutane kimanin dubu 30 suka halaka sakamakon abin da ya biyo bayan haɗarin ma'aikatar sarrafa maganin ƙwari a Bhopal ta ƙasar Indiya

Abin da ya rage daga masana'antar maganin kashe ƙwari ta Union Carbide a Bhopal

A fafutukarsu ta neman cin ƙazamar riba manyan kamfanonin ƙasashen ƙetare kan zuba jari a ƙasashe masu rafusan albashin ma'aikata a Afirka ko Asiya. A baya ga haka kamfanonin kan yi sako-sako da matakan kariya ga ma'aikata da kewayen ɗan-Adam. Hakan ma dai na ɗaya daga cikin musababbin haɗarin da ya faru a masana'antar sarrafa magungunan ƙwari ta Union Cabride dake Bhopal a ƙasar Indiya, wanda a sakamakonsa mutane sama da dubu 30 suka halaka

Bisa ga dukkan alamu dai har yau ba a koyi darasi daga wannan mummunan hatsarin da ya afku a masana'antar sarrafa magungunan kashe ƙwarin ta kamfanin Union Carbide ɗan ƙasar Amirka a misalin shekaru 25 da suka wuce ba. An saurara daga wani mai fafutukar kare kewayen ɗan-Adam Chandra Bhushan yana mai faɗi cewar:

"Duk da mummunan hatsarin da ya wakana a Bhopal har yau babu wani takamaiman matakin tsaron da aka gabatar. Musamman a ƙasar Indiya, kusan a kullu-yaumin sai an fuskanci wasu 'yan ƙananan haɗaruruwa. Kullum sai mun samu labarin haɗaruruka, inda a yau za a ce mutum biyu sun mutu, gobe a ce wasu mutane huɗu sun rasa rayukansu."

Chandra Bhushan ɗan wata ƙungiya ce dake fafutukar kare kewayen ɗan-Adam a New Delhi, fadar mulkin ƙasar Indiya. Ya ce ko da yake bayan afkuwar haɗarin gwamnati ta gabatar da wasu dokoki amma basu da tsanani kuma wasu 'yan ƙalilan ne daga cikinsu aka aiwatar.

"An tsaurara wasu dokoki bayan afkuwar haɗarin, amma matsalar ita ce an gaza wajen aiwatar dasu. Kazaklika an gaza wajen neman cikakkiyar diyya daga kamfanin dake da alhakin lamarin. Wajibi ne idan har an sake fuskantar wani haɗari irin shigen na Bhopal a ɗauki matakai akan masu alhakin lamarin. Sau tari wasu 'yan ƙananan haɗaruka kan faru amma ba a ɗaukaka ƙara kan masu alhakin lamarin. A sakamakon haka suke wa maganar riƙon sakainar kashi."

A haƙiƙa dai neman ƙazamar riba da gudanar da ayyukan samarwa a cikin rafusa, shi ne ainihin abin dake jan hankalin manyan kamfanonin ƙasashe masu ci gaban masana'antu su zuba jari a nahiyar Afirka, in ji Nick Guroff daga wata ƙungiyar Amirka mai zaman kanta dake fafutukar neman diyya daga manyan kamfanoni na ƙasa da ƙasa.

"Abin takaicin dake ci gaba da ci mana tuwo a ƙwarya dangane da haɗarin Bhopal shi ne, waɗannan manyan kamfanoni su kan zuba jari ne a wuraren da ba a da wasu tsauraran sharuɗɗa ko wasu dokoki na kare haƙƙin ɗan-Adam. Su kan yi amfani da wannan dama domin rage yawan abin da suke kashewa a ayyukansu na sarrafawa da kuma hanƙoron ƙazamar riba. Ɗaukar hankalin da haɗarin na Bhopal yayi shekaru 25 da suka wuce ya zama muhimmin gargaɗi ga kamfanonin su zan da sani cewar za a ci gaba da samu ƙungiyoyi na farar hula, waɗanda zasu riƙa fito da irin wannan taɓargaza a bainar jama'a a kuma ɗauki matakin da ya dace akan kamfanonin a ƙasashensu."

Nick Guroff ya ƙalubalanci iƙirarin da kamfanonin ke yi na cewar ba kawai riba ce ke kai su ƙasashe masu tasowa ba, suna kuma taimakawa wajen samar da guraben aikin yi ga jama'a da ba da kafar samun ilimi ga matasa. Nick ya ce wannan zance ne na kawai. Wajibi ne mutum ya amince da kurakuransa ya taimaka wajen kare haƙƙin ɗan-Adam amma ba maganganu na fatar baki kaɗai ba.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu

Ƙari daga wannan rukuni