1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duniyar ɗan Adam

Damuwa mai tsanani tsakanin Bil'adama

Ana iya cewar damuwa mai tsanani wani nau'i ne na rashin lafiya?

Robert Enke

Kashe kansa da mai tsaron gida na ƙungiyar kwallon kafa ta tarayyar Jamus Robert Enke yayi a kwanakin nan, ya haifar da ayar tambaya dangane da matsaloli da mutane kan tsinci kansu a ciki sakamakon damuwa mai tsanani, da kuma yadda suke taryar lamarin.

Sakamakon binciken da masana halayyar ɗan Adam suka yi yayi nuni dacewar, a kalla kashi 10 na maza da kuma 20 daga cikin 100 na mata, dake nan tarayyar Jamus ne ke fama da matsalar damuwa mai zurfi.

Bincike yayi nuni dacewar a kowace rana akalla jamusawa miliyan huɗu ne ke rayuwa da manyan alamomin wannan matsalar, wadda ake bayyanawa da wani nau'i na rashin lafiya. Duk kuwa dacewar ba za a iya cewa rashin lafiya ce kai tsaye ba.

A yanzu dai ana kallon wannan matsalar tankar wani nau'i ne na rashin lafiya da mutane ke fama da shi, fiye da yadda ake masa kallo a baya. A dalilin irin wannan damuwa mai tsanani nema, ya haddasa akan bar mutane suyi murabus daga bakin aiki, kafin shekarunsu na barin aiki yakai.

Sai dai ba dukkan mutane kanyi tawakalli da wannan matsala ta kasancewa a cikin damuwa mai tsanani, domin wasu bazasu iya jurewa ba, wanda ya kan jagorance su zartar da hukuncin kashe kansu kamar yadda Robert Enke yayi.

Professor Mathias Berger, shine Direkta a sashin kula da halayyar ɗan Adam, da masu taɓin hankali a asibitin horarwa na jamiar Freiburg dake nan Jamus, kuma acewarsa al'amarin ya banbanta.

Mathias Berger

" akwai wasu mutane da yanayin halittarsu takeda karfi, waɗanda larularsu kan danganci sauyin yanayin lokaci, kamar bazara ko sanyi ko kuma damuna. Akwai kuma wasun da sai fuskanci damuwa mai tsanani kafin su yi rashin lafiya. Sai abun farin ciki shine, mafi yawa daga cikin mutane basa yarda komin tsananin yanayi yasa su cikin damuwa"

Mutun zai iya tsintar kanas cikin yanayi na damuwa mai tsanani a kowane shekaru. Sai dai anfi samun masu fama da wannan nau'i na rashin lafiya ne a rukunin mutanenda suke tsakanin shekaru 30 zuwa 40.

Kazalika an gano cewar kaɗaici, da yawan ɓacin rai ko kuma tashin hankali yakan jagoranci mutum zuwa damuwa mai tsanani.

Al'amari na runguman kaddara dai yakan jagoranci zartar da hukun kisan kai, wanda a wasu lokuta a ɓangaren mazan, mata ne umul'abaisin hakan, sai dai ya zamanto kuma sune sukafi matan salwantar da rayukansu.

Makokin Enke

Matsalar dai babu yadda bata zuwa kama daga rashin iya barci, ko kuma idan kayi barci sai kayi saurin tashi.Amma acewar Professor Bergers, anan ma abun ya banbanta..

" akwai abunda za a iya bayyanawa da kasancewa damuwa mai tsanani na maza. Hakan na nufin kaga mutun cikin kuzari a koda yaushe, a ɓangaren harkokin wasannin ne, da dai sauransu,idan mutun ya nemi taimaka musu da wani abun ,sai suce basa neman wani taimakao, domin su kaɗai suka kai inda suke a ayau"

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Abdullahi Tanko Bala

Ƙari daga wannan rukuni