Wasu dattawan Najeriya bisa jagorancin Farfesa Wole Soyinka sun shigar da kara kotu domin ta haramta kundin tsarin mulkin kasar
Wole Soyinka
A baya dai sun yi kaurin suna wajen bullo da dabarun neman sauyi a bisa tsari dama fasalin da suke fatan ganin tarrayar Najeriya bisa kai. Sun ma kai ga kafa kungiyoyi da kiran taruka duk dai a kokarin neman cika burin nasu.
To sai dai kuma daga dukkan alamu suna shirin sauya sallo ga wasu manyan jiga jigan tarrayar Najeriyar da yanzu haka ke kotu da nufin neman rushewar daukacin kundin tsarin mulkin da kasar ke tafiya kansa.
Karkashin jagorancin farfesa Wole Soyinka dai, dattawan sun nemi wata kotun tarraya da ta bayyana kundin tsarin kasar na shekara ta 1999 a matsayin wanda sojan kasar suka tilasta kan jama'arta kuma ke zaman haramtacce a garesu.
Maraba da zuwa Abuja
Sabuwar dabarar da yanzu haka kotun ke dubawa dai na zaman ta baya baya a kokarin ganin bayan kundin da tsohuwar gwamnatin General Abdu Salam Abubakar ta barwa al'ummar kasar da kuma 'yan siyasa su kayi nasarar yiwa kwaskwarima a kalla sau biyu.
To sai dai kuma daga dukkan alamu kokarin ganin bayan kundin dai na shirin bude sabuwar mahawara a tarrayar Nijeriya kasar da yanzu haka ke fuskantar rarrabuwa, sakamakon rigingimun siyasa da kuma zamantakewa a tsakanin sassanta daban-daban.
Shi kansa kundin dai ya tanadi duk wani gyara kansa ya kasance ya fito daga majalisun dokokin tarraya da jihohin kasar 36, abun kuma da a cewar senata Ahmed Lawan da a baya ya taka rawa wajen kokarin gyare-gyaren ,bai sauya ba har ya zuwa yau.
Fadar mulkin Najeriya
Samun wakilci ko kuma watsi da kayan soja dai babban burin datawan da yanzu haka ke tsugune gaban kuliyar na zaman warware zare da abawar wakilci a tsakanin tsarin sojan da ba zabar sa aka yi bad a kuma na demokaradiyar da Nijeriyar ke tafiya kai yanzu.
Duk da karfin tuwon da ke akwai ga mulkin na soja dai , sashe daya karamin sashe na 93 na dokar soja ta 1999 da ta haifar da kundin dai ta fara ne da” mu 'yan Najeriya “ abun da kuma ya saba da yanayin da ya kai ga haihuwar kundin.
To sai dai kuma a cewar Barrister Waziri Yushua Mamman dake zaman wani lauya mai zaman kansa a nan Abuja, wakilcin kwamitin da ya samar da kundin karkashin mulkin na soja hallastacce ne kan kowa.
A ranar 15 ga watan gobe na Maris dai ne aka tsara cigaba da shari'ar da tazo dai dai da kiraye-kirayen neman sake fasalin daukacin kasar ta Nigeria da kuma a keyiwa kallon alamu ta kama hanyar farkon karshen kasar da ta share shekaru 50 din farko na 'yancin kanta cikin rudani na kabilancin kudu da arewa.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Yahouza Sadissou Madobi