1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 41 magoya bayan Gaddafi sun gurfana gaban kotun soji

A matakin farko na shari'ar magoya bayan Gaddafi an gurfanar da mutane 41 a gaban kotun soji a Benghazi.

The head of Libya's rebel Provisional Transitional Council Mustafa Abdul Jalil, speaks during a presser conference where he offered to implement a ceasefire with Libyan leader Moamer Kadhafi on condition Kadhafi's forces withdraw from besieged western cities and freedom of expression is allowed across the country in Benghazi on April 01, 2011, after meeting with the UN special envoy to Libya Abdul Iliah Khatib. AFP PHOTO/Marc Burleigh

A ƙasar Libya a yau aka gurfanar da mutane 41 magoya bayan tsohon shugban Libya Muammar Gaddafi a gaban kotu a matakin farko na shari'ar mambobin tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe. Mutanen da aka gabatar gaban kotun waɗanda yawancinsu farar hula ne sun baiyana ne a gaban kotun soji a gabashin birnin Benghazi birnin da aka fara zanga zangar adawar wadda ta kai ga hamɓarar da gwamnatin Gaddafi dama kuma hallaka shi a mahaifarsa birnin Sirte. Alƙalin kotun kanar Ali al-Hamida a yayin da mutanen suka baiyana a gabansa, ya yi tsokaci da tarzomar juyin juya halin wadda ta faro a ranar 17 ga watan Fabrairun bara a birnin Benghazi. Ana zargin mutanen ne da taimakawa gwamnatin Gaddafi a yunƙurinta na murƙushe masu bore da taimakawa fursunoni tserewa daga gidan yari sannan kuma da zargin kafa ƙungiyoyin 'yan ta'adda. Rahotanni sun ce an gudanar da zaman farko na kotun cikin tsauraran matakan tsaro. Sai dai lauyoyi goma sha biyar da ke kare waɗanda ake tuhuma sun yi ƙorafin cewa dukkan mutanen farar hula ne amma kuma ana tuhumar su a gaban kotun soji, matakin da suka ce bai dace ba.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal