1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages
Onlookers  gather around a car destroyed in a blast next to St. Theresa Catholic Church in Madalla, Nigeria, Sunday, Dec. 25, 2011. An explosion ripped through a Catholic church during Christmas Mass near Nigeria's capital Sunday, killing scores of people, officials said. A radical Muslim sect claimed the attack and another bombing near a church in the restive city of Jos, as explosions also struck the nation's northeast. (Foto:Sunday Aghaeze/AP/dapd)

Siyasa

Kungiyar Boko Haram ta yi zargin yaudara

Barazana ga kokarin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya

A wani abun dake zaman kara fuskantar yanayi maras tabbas a rikicin da yanzu haka ke tsakanin gwamantin tarrayar Najeriya da kuma 'ya'yan kungiyar Boko Haram mai fafutuka da bama bamai, kungiyar data zargi mahukuntan kasar da yaudara,  tace ba zata shiga duk wata tattaunawa da gwamantin kasar ba har sai an saki daukacin 'ya'yan ta dake tsare.  Karar bindigogi kenan a wani bikin faretin kuratan soja a birnin  Zariya a sashen arewacin tarrayar Najeriya  ranar Jumma'a , a wata alamar dake nuna irin karfin hatsi na sojan kasar da yanzu haka ke kan gaba a yaki da 'ya'yan kungiyar Boko Haram.

Yakin kuma da sannu a hankali ke neman komawa ya zuwa kafafen yada labaran kasar  da ma na wajenta da suka dauki kusan kwanakin  ukun karshen makon da muke ciki,  suna kallon sabuwar dambarwar dake tsakanin gwamantin Najeriyar da yayan kungiyar ta Boko Haram. A cikin tsakiyar makon ne dai majiyoyin tsaron Najeriya suka bada tabbacin kame wani da suka ce kakain kungiyar ne Abul Qaqa a birnin Kaduna, bayan wani samamen da suka ce sun yi amfani da naurorin zamani a wajen kaishi.

Wer hat das Bild gemacht?: Babangida Jibril
Wann wurde das Bild gemacht?: 07.12.2011
Wo wurde das Bild aufgenommen?: Kaduna / Nigeria
Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? 
Schaulustige, Leute und Sicherheitskräfte bei einer Explosion, die sich auf einem Markt in der zentralnigerianischen Stadt Kaduna ereignet hat.

Hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram

Kamun daga baya kuma Boko Haram  din ta fito tace mutumin da aka kama din ba kakakin ta bane face wani jigon wayar da kan al'ummar ta  ne dake da lakabin Abu Darda wanda tace ta tura can ne domin bude tattaunawa tsakanin ta da mahukuntan kasar ta Najeriya. Duk da cewar dai har ya zuwa yanzu  jamian tsaron da suka ce suna binciken jigon sun ki Karin haske game da ko shi wanene balle rawar da yake takawa a cikin aiyyukan kungiyar mai fafutuka da bama bamai. Kamen nasa dai daga dukkan alamu na shirin jefa kokarin kasar na sulhu da 'ya'yan kungiyar cikin tsaka mai wuya.

Tuni dai wani daya ce shine Abul Qaqa na gaskiya, yace kungiyar tasu  dake zargin gwamantin da yaudara ta tsaida duk wani kokari na neman sulhu har sai an kai ga sakin Abu Dardan, dama duk wani dan kungiyar dake hannu zuwa yanzu.  Matsayin kuma da daga dukkan alamu ke iya kawo cikas ga gwamantin da tun da farko shugabanta ya aiyyana aniyar sa ta tattaunawa da 'ya'yan kungiyar in har ta gano ku su wanene. Daruruwan 'ya'yan kungiyar ne dai ke kurkuku a sassa daban daban na arewacin Tarrayar Najeriyar inda ake zargin su da ta hankali da kokarin zub da jini.

Mallam muhammaed sule dai wani masharhanci ne kan batun na tsaro a nan Abuja.

epa03046191 (FILE) A file photograph Goodluck Ebele Jonathan, President and Commander-in-Chief of the Armed Forces of the Federal Republic of Nigeria speaks during the general debate at the 66th session of the United Nations General Assembly at United Nations headquarters in New York, New York, USA, on 21 September 2011. Media reports state on 31 December 2011 that President Goodluck Jonathan has declared a state of emergency in areas affected by attacks from the Islamist group Boko Haram. Borders will be temporarily closed in the north-eastern states of Yobe and Borno, and central state of Plateau. EPA/JASON SZENES *** Local Caption *** 00000402928322 +++(c) dpa - Bildfunk+++

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

To sai dai kuma ko ya take shirin kayawa a tsakanin Abu Dardan da 'yan uwansa 'an kungiyar ta Boko Haram a waje daya,  sannan kuma da mahukuntan kasar da ke fatan kawo karshen zub da jinin kasar ta Najeriya a cikin sauri dai, wani sabon kalubalen dai na zaman wani rikicin cikin gidan da yanzu haka ya kai ga kisan wasu 'ya'yan kungiyar shida, sannan kuma ke barazanar raba kanta gida biyu.

Akkalla mutane shida da ake kyautata zaton  'ya'yan sabon bangaren  ne na Boko Haram aka yiwa yankan rago a garin Maiduguri a ranar Alhamis a wani abun dake zaman yakin cikin gida a tsakanin bangarorin biyu dake zargin junan su da tona asiri.

Rabuwar kan 'ya'yan kungiyar dai na kuma iya raba hanakalin gwamnatin dake fatan kawo karshen rikicin a cikin sauri ga Najeriya da tayi asarar mutane sama da 500 a cikin tsawon watani biyu na farkon shekarar da muke ciki.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin