1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

sabuwar mai gabatar da ƙara ta kotun duniya

An zaɓi mace ta farko 'yar Afirka daga ƙasar Gambiya a matsayin babbar mai gabatar da ƙara ta kotun ƙasa da ƙasa dake Hague. Lauya Fatou Bensouda za ta maye gurbin Luis Moreno - Ocampo ɗan ƙasar Argentina

Fatou Bensouda, sabuwar mai gabatar da kara ta kotun duniya

Fatou Bensouda

A ranar Litinin da ta gabata ce a birnin New York wakilan ƙasashe da suka sanya hannu a yarjejeniyar Rome ta kafa kotun duniyar suka zaɓe ta akan wannan matsayi daga cikin 'yan takara huɗu da suka nemi muƙamin.

Fatou Bensouda na iya bugun ƙirgi da alfahari kan gogewar da ta samu a matsayin ƙwarariyar lauya. A saboda haka ne ma tsawon lokaci ta zama mataimakiyar babban mai gabatar da ƙara na kotun duniyar da ke Hague wato Moreno - Ocampo, muƙamin da ta ke riƙe da shi tun a shekarar 2004. Ƙwarewarta da kuma gogewar da ta samu a an aikin kotun ta ƙasa da ƙasa sun taimaka mata samun wannan sabon matsayi. Wajibi ne mutum ya nuna sanin makama a wannan aiki, ta yi imanin cewa aikin kotun ta ƙasa da ƙasa mai shari'ar manyan laifuka ya taimaka wajen rage aikata laifukan cin zarafin al'uma musamman a nahiyar Afirka. " Ta ce waɗanda suka tsara daftarin kundin Rome sun hango dangantaka mai ƙarfi da ke akwai tsakani adalci da zaman lafiya. Ta hanyar kawo ƙarshen izgilancin masu aikata manyan laifuka, kotun za ta iya kuma ma ta taimaka wajen rage aukuwar waɗannan laifuka ta hanyar zama ishara ga wasu".

A lokacin da ta kasance shugabar kotun musamman ta laifukan yaƙi na ta'asar kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a birnin Arusha, kafin ta fara aiki da kotun ta ICC ta jagoranci binciken laifuka da dama. Bayan da ta kammala karatun lauya a Najeriya a shekarar 1987, ta fara aiki a matsayin mai gabatar da ƙara kana likafa ta yi gaba ta zama babbar mai gabatar da ƙara, ta riƙe dukkan waɗannan muƙamai ne a ƙasarta ta haihuwa. Ta sami digirinta na biyu a fannin dokoki da suka shafi harkokin sufurin jiragen ruwa a ƙasar Malta, inda ta kasance ƙwararriya ta farko a fannin dokokin sufurin jiragen ruwa a ƙasar Gambiya.

Zaman kotun duniya

Kasancewarta 'yar Afirka Fatou Bensouda ta sami zama mataimakiyar Moreno Ocampo cikin sauƙi, saboda mafi yawancin ƙararrakin dake gaban kotun sun shafi akasarin 'yan Afirka ne. A saboda haka naɗinta a kan wannan matsayi bama kawai zai ƙarawa kotun ta ICC martaba bane kaɗai zai ma sauya tunanin da wasu ke yi cewa kotun ta fi hararar shugabanin Afirka ne kawai kamar yadda Farfesa Kai Ambos daraktan cibiyar nazarin dokokin ƙasa da ƙasa a jami'ar Goettingen yake cewa " Kasancewar ta san ciki da wajen harkokin gabatar da ƙara, ya sa ta zama mataimakiyar Ocampo, ta kuma san irin kura kuran da ya aikata, a saboda haka za ta gyara har ma ta yi aiki fiye da shi. Ta na da ƙima a idanun jama'a a saboda haka ana martaba ta, mace ce mai kamala wadda kuma ta san hulɗa da jama'a".

Su ma dai ƙasashen Afirka waɗanda suka amince da kotun ta ƙasa da ƙasa sun yaba inda suka sha baiyana fatan ganin an sami mai shari'a ɗan Afirka wanda ya san al'amuran Afirka a tsarin gudanarwar kotun. Sai dai a hannu guda 'yan Afirka da dama na baiyana damuwar su cewa shugabannin Afirka ne kaɗai ake gurfanarwa a gaban kotun. Wasu ma na zargin cewa kotun ta zama wata kafa da turawan yamma ke amfani da ita wajen gallazawa shugabannin Afirka waɗanda basa ɗasawa da su, zargin da Fatou Bensouda ta musanta " Ina mamakin yadda za'a yi zargin cewa kotun na fakon 'yan Afirka ne, gwagwarmayar da ake yi na yaƙi da izgilanci ba wani salo ne na mulkin mallaka ba, hasali ma kotun ta sami amincewa da goyon bayan a'uma a nahiyar Afirka".

Ƙasar Senegal ita ce ƙasar Afirka ta farko da ta sanya hannu a shekarar 1999 akan yarjejeniyar Roma ta kafa kotun ta ƙasa da ƙasa tun daga sannan kuma sauran ƙasashen na Afirka suka biyo baya. A yau akwai ƙasashen Afirka fiye da 30 waɗanda suka amince da kotun kuma kashi ɗaya bisa uku na alƙalan kotun 'yan Afirka ne.

Mawallafa: Lina Hoffmann / Abdullahi Tanko Bala
Edita: Zainab Mohammed Abubakar