1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Kasashen dake amfani da Euro

A shekara 1999 aka rattaba hannu kan yarjejeniyar amfani da Euro.A halin yanzu Kasashe 17 ke amfani da Euro.

Kasashe nawa ke amfani Euro?

Baki daya a halin da ake ciki yanzu kasashe 17 ke amfani da takardar kudi ta Euro.

A shekara ta 2002 aka fara amfani da Euro.

Amma tun 1999 ,kasashe 11 suka cimma yarajejeniyar amfani da wannan kudi, kasashen kuwa sune Jamus, Faransa, Austriya,Beljiam,Spain,Finland,Irland,Luxemburg,Holland, Italiya da Portugal.

Daga bisani sauran kasashe suka biyo baya, Girka ta shiga a shekara 2001, Sloveniya a shekara 2007, tsibirin Malta da Siprus a 2008, Slovakiya ta shiga a shekara 2009.

Kasa ta baya-bayan nan wadda ta shiga Euro itace Estoniya a farkon shekara 2011.

Saidai yanzu haka akwai kasashe da dama na Turai masu zawarcin samun matsayin memba a cikin rukunin masu amfani da Euro, duk kuwa da matsalolin tattalin arziki da wannan kasashe ke fama da su.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal