1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages
DW Sprachkurse Deutsch warum nicht Brandingbanner Deutsche Welle, Sprachkurse/Bildungsprogramme, (c) DW Auslandsmarketing 2012, Benutzung nur für Deutschkurse!

Jamusanci - Me zai hana ka koyonsa?

Kashi na daya

Aachen - Hotel Europa. Andreas yana aiki a wannan otel, bayan karatun sa na aikin jarida. Wannan aiki ne mai matukar ban sha'awa. Wani lokaci otel din yakan zama mai damuwa, wani lokaci baki a otel din sukan nemi wasu bukatu masu ban mamaki, ko kuma sanannen mawakin nan dake daki mai lamba 10, wanda ba zato ba tsammani ya bace. Akwai fannoni masu muhimmanci na nahawu. Wannan kashi na farko ya kunshi darussa 26.

Matakin farko

Jamusanci - Me zai hana ka koyonsa?

Andreas yana son zama dan jarida. Wajibi ne ya samu dan abin masarufi a lokacin da yake koyon wannan sana'a ta hanyar aiki a wani otel a matsayin mai karbar baki da tsaron kofa. Ku bakunce mu a wannan otel dake birnin Aachen, ku koyi Jamusanci tare da Andreas da wani bako da kann sauka a otel din, mai suna Dr. Thürmann da mai sharan dakunan otel, Hanna Claasen da kuma abokiyar tafiyar Andreas mai ban mamaki da ake kira Ex. Idan har kuna da ilimin harshen Jamusanci a matakin farko, kai tsaye kuna iya shiga kashi na ukku da na hudu - Me zai hana ka koyon sa? A can, zaku ga an maimaita labarai dake kashi na farko da na biyu .

German courses