1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages
  • Kofar shiga Turai

    Baƙin haure a Lampedusa

    Kofar shiga Turai

    Tun farkon shekarun 1980 tsibirin Lampedusa ya ƙofar shiga nahiyar Turai ga baƙin hauren Afirka da na Gabas Ta tsakiya. Kwarararsu ta yi ta ƙarunwa a cikin shekaru 10 da suka wuce, abin da ya kai ƙololuwa biyo bayan iskar canji da ta kaɗa a ƙasashen Larabawa a 2011. A bara baƙin haure 28,000 daga Tunisiya aka ƙiyasce sun shigo Turai ta tsibirin na Lampedusa.

  • 'Tsaunin kunya'

    Baƙin haure a Lampedusa

    'Tsaunin kunya'

    Rashin tanade tanade na karɓar baƙin hauren Tunisiya - biyo bayan kifar da shugaba Ben Ali a watan Janerun 2011 - ya sanya baƙin ahuren da kansu kafa wani sansanin wucin gadi marsa kyau a kan wani tsauni dake kallon tshar jirgin ruwa. Mazauna tsibirin sun kira shi "tsaunin kunya".

  • Gwajin sa'a na dindindin

    Baƙin haure a Lampedusa

    Gwajin sa'a na dindindin

    Ana cika ƙananan kwalalen kamun kifi da ɗaruruwan mutane musamman cikin dare don kauce wa idanun masu tsaron gaɓar tekun Tunisiya. An saye da yawa daga cikin kwallelen ne daga masunta wasu kuma an sace su ne idan masunta suka ƙi. Farashin wannan gwajin sa'a ya kama daga euro 1500 zuwa 2000.

  • Yada zango maras ƙarewa

    Baƙin haure a Lampedusa

    Yada zango maras ƙarewa

    Ga baƙin hauren, Lampedusa na matsayin Italiya sannan Italiya kuma na zama ƙofar shiga Turai. Sai dai da zarar sun isa tsibirin sai su yi na dama. Taƙaddama tsakanin Italiya da EU ya janyo kafa wata gurguwar manufar 'yan gudun hijira da suka tagaiyara. Hakan ya kasance farkon shiga wani yanayin rashin sanin tabbas ga baƙin hauren.

  • Kwana kan titi

    Baƙin haure a Lampedusa

    Kwana kan titi

    Ya zuwa ƙarshen watan Maris 2011, yawan baƙin haure ya fi na mazauna tsibirin Lampedusa. Duk da takaici da fushin haka, mazauna tsibirin sun ci gaba tarbar baƙin da hannu bibiyu inda suka riƙa ba su barguna da abinci. Wannan dai na da muhimmanci kasancewa dubban baƙin ba su da wurin kwana tsawon makonni.

  • Bala'i cikin wani bala'i

    Baƙin haure a Lampedusa

    Bala'i cikin wani bala'i

    Yayin da rikicin ya kai ƙololuwa, kace nace na siyasa tsakanin Italiya, EU Tunisiya ya shiga mummunan hali. Baƙin haure sun kasance a wani filin Allah ta'ala, ba tare da abinci da wurin kwana ba. A daidai lokacin na masu zuwa yawon buɗe ido, otel-otel sun sanar da rashin kasuwa.

  • Shawagin jiragen sama

    Baƙin haure a Lampedusa

    Shawagin jiragen sama

    A farkon watan Afrilu, ma'aikatun cikin gidan Italiya da Tunisiya sun cimma yarjejeniyar dakatar da kwararar baƙin daga Tunisiya zuwa Lampedusa. An ba wa Italiya 'yancin komawa da baƙin hauren da ƙarfi, abin da ke nufin matasan da suka biya maƙudan kuɗaɗen kuma suka sanya rayukansu cikin kasada suka tsere daga Tunisiya, za a koma da su gida.

  • Asarar rayuka

    Baƙin haure a Lampedusa

    Asarar rayuka

    Juyin juya halin da ya faru a Tunisiya a watan Janerun 2011, shi ne mafarin iskar canji da ta kaɗa a ƙasashen Larabawa. Mutane kimanin 60,000 ba su san makomarsu ba, a lokuta da dama suna mutuwa a tekun Bahar Rum akan hanyarsu ta zuwa Turai ta tsibirin Lampedusa. Har yau dubbai na tashi daga Libiya da Tunisiya zuwa Turai.

  • Korar baƙi

    Baƙin haure a Lampedusa

    Korar baƙi

    A ƙarshen watan Maris 2011, an fara tura jirgin ruwan yaƙin Italiya zuwa Lampedusa don fara kwashe dubban 'yan Tunisiya da suka tagaiyara. An tura su zuwa sansanoni dake cikin Italiya. Waɗanda ba su da dangi a Turai ko kuɗin ɗaukar nauyin kansu an koma da su Tunisiya.

  • Baƙin sashe na juyin juya halin Larabawa

    Baƙin haure a Lampedusa

    Baƙin sashe na juyin juya halin Larabawa

    Bayan kwararar baƙin farko, an yaɗa labarin cewa masu tsaron gaɓar tekun Tunisiya da Italiya za su rufe hanyar shiga Lampedusa. Amma jin kaɗan bayan boren Libiya a Febrerun 2011, ba a ga ƙarshen baƙi da 'yan gudun hijira Lampedusa ba. Daga cikin mutane 60,000 da aka ƙiyasce sun tsallake tekun Sicilly, fiye da 2,000 suka rasa rayukansu a cikin teku.

  • An rufe

    Baƙin haure a Lampedusa

    An rufe

    A Satumban 2011, wani gungun 'yan gudun hijira sun cinna wuta a cibiyar karɓar baƙi a Lampedusa. Lamarin ya sa an tuna da halin da aka shiga farko a tsibirin. Italiya ta yi kira da a rufe cibiyar har abada. Har yanzu wannan cibiya tana rufe.

  • Tura ta kai bango

    Baƙin haure a Lampedusa

    Tura ta kai bango

    Italiya ta ayyana Lampedusa da cewa bai dace da tsaron baƙin haure ba. Hakan ya rage yawan bakin dake shiga tsibirin. Sai dai an yi aikata ta'asa. Wani mai shirya fim na labari ɗan Italiya ya ce ya ga hukumomin Italiya suna muzguna wa wasu baƙi a cikin jirgin saman Alitalia. Hukumomin Italiya sun yi watsi da wannan zargi.


    Mawallafi: Gaia Anderson | Edita: Mohammad Awal

SHIRYE-SHIRYE

Rediyon DW koyaushe a cikin kunne

ALBISHIR: Kuna iya sauraron shirye-shiryen DW a harsunan Afirka guda shida kai tsaye (hausa, swahili, amharik, ingilishi, faransanci, harshen Portugal) a duk lokutan da aka saba. Idan sun wuce ku, kuna iya sauraren shirye-shiryen Hausa ta „Audio on demand“! Kuna iya zaben abin da za ku saurara daga jerin shafunan dake kasa.

Kuna iya tuntuɓarmu akan wannan adireshi: hausa@dw.de ko kuma ku aiko mana da gajeren saƙo akan wayarmu mai lamba: +49-173-7100428