1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dole a magance matsalar ci-rani tun daga tushe

Mohammad Nasiru AwalApril 24, 2015

Mace-macen 'yan gudun hijirar Afirka da ke bi ta tekun Bahar Rum don shigowa Turai suka mamaye sharhi da labaran da jaridun Jamus suka yi game da nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/1FEJH
Italien Migranten
Hoto: picture-alliance/dpa/Italian Navy Press Office

A labarin da ta buga jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce Afirka na fuskantar bunkasar al'umma Turai kuma ta zama tamkar maganadisu ga 'yan gudun hijira da ke tserewa daga rikice-rikice a kasashe irinsu Siriya da Libiya da ma wasu kasashen Afirka Kudu da Sahara. Jaridar ta ce hanya mafi dacewa wajen kawo karshen wannan bala'i na 'yan gudun hijira da ke daukar kasadar bi ta tekun Bahar Rum don shigowa Turai, shi ne magance tushen matsalolin da ke tilasta su yin kaura ko dai a kasashensu na asali ko a kasashen da suke yada zango ciki, musamman ma matsalolin siyasa da na tattalin arziki.

Bala'i ga duniya baki daya

Italien Flüchtlinge in Lampedusa
'Yan ci-rani a LampedusaHoto: Reuters/A. Bianchi

Ita kuwa a sharhin da ta yi mai taken Bala'i da ya shafe-mu mu duka, jaridar Berliner Zeitung cewa ta yi tun bayan asarar daruruwan rayukan 'yan ci-rani a tekun Bahar Rum a karshen mako aka sake ta da mahawara kan inganta yanayin rayuwa a kasashen da 'yan gudun hijirar suka fito. Wannan dai ba shi ne karon farko da ake irin wannan mahawara ba, amma da zarar abubuwa sun lafa sai ka ji shiru har sai an sake samun aukuwar wani bala'in. Ba wai Turai ba ta da karfin taimakawa ba ne, abin da take rashinsa shi ne wani kuduri da aniyar taimakawa. Bai kamata mu yaudari kanmu, gaskiyar magana ita ce muna matakin farko shiga wata tururuwar 'yan gudun hijira a Turai, wadanda ke tserewa daga yake-yake da tursasawa da rashin sanin makoma. Matakin farko shi ne nahiyar Turai ta fara sabon shirin ceto a teku, ta samar da hanyoyin halal na shigowa Turai sannan a ci gaba da daukar matakan inganta rayuwar mutane tare da magance tushen matsalolin da ke janyo yin kaurar.

Hukumar WHO ta koyi darasi

Daga batun 'yan ci-ranin sai na kiwon lafiya, inda jaridar Der Tagesspiegel ta rawaito cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta koyi darasi daga annobar Ebola.

Guinea MSF Ärzte ohne Grenzen Einsatz gegen Ebola
Ana bukatar inganta matakan riga-kafiHoto: Amandine Colin/Ärzte ohne Grenzen

Ta ce bayan da cutar Ebola ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 10,000 a yammacin Afirka, shugabannin WHO sun soki kansu da kansu bisa abin da suka ce an makara wajen daukar matakan gaggawa. Saboda haka ya zama wajibi duniya ta zama cikin shirin ko ta-kwana idan wata tsohuwar annoba ta barke amma da wata siga ta daban. Hukumar ta lafiya ta ce ana bukatar wani sabon tsarin tinkarar cututtuka domin samar da magunguna da allurar riga-kafi musamman masu amfani ga talakawa. Duk da haka hukumar ta yaba da kokarin da duniya ta yi kuma ta ce nan gaba za a karfafa hadin kai.

Afirka ta Kudu ta bashe da 'yan Afirka

Tsoffin abokan kungiyar ANC sun ji takaicin boren kyamar baki a kasar Afirka ta Kudu inji jaridar Die Tageszeitung tana mai cewa a karshen mako shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya nuna kaduwa da jin haushi dangane da hare-haren kyamar baki da 'yan Afirka ta Kudu ke kai wa baki daga wasu kasashen Afirka da ke zaune a kasar. Su ma masharhanta a ko ina cikin Afirka sun nuna rashin jin dadinsu ga wannan al'amari musamman kasancewa kasashen Afirka ne suka kawo wa bakaken fatan Afirka ta Kudu goyon baya lokacin mulkin wariyar launin fata.