1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Darasi daga kisan kiyashin Ruwanda a 1994

April 11, 2014

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan bikin juyayin cikar shekaru 20 da kisan kare dangin da aka yi a kasar Ruwanda.

https://p.dw.com/p/1BgPy
Ruanda Genozid Gedenken 07.04.2014
Hoto: Reuters

A labarinta mai taken darasi daga Ruwanda jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi.

„Cibiyoyi da wuraren tunawa da kisan kare dangin shekarar 1994 a Ruwanda suna da yawa, sai dai wasu sun fi wasu daukar hankali, musamman na wuraren da aka ajiye kokon kawunan da sauarn kwarangwal mutane da aka yi wa kisan kiyashi. Duk wanda ya ziyarci wadannan wuraren tambayar da zai fara yi wa kansa ita ce-mai ya hana a dauki matakan hana wannan ta'asa aukuwa? Ba wai gamaiyar kasa da kasa ba ta yi komai ba ne a 1994, sai dai kasashen da suka yi wani abu don hana wannan ta'asar, sun tabka kurakurai, musamman na rashin daukar matakan da suka dace a kuma lokacin da ya dace. Jawaban da aka albarkacin zagayowar shekaru 20 da kisan kiyashin a Ruwanda sun aike da sakon xcewa akalla duniya ta koyi darasi daga wannan ta'asa. Kuma ana iya ganin wani ci gaba daga bangaren kasashen Afirka, inda kungiyar AU ta sake fasalta kanta ta yadda za ta iya kai dauki a kasashe membobinta. Ga misali a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda sojojin sa kai na Kirista da Musulmi ke yi wa juna kisan gilla, kungiyar ta girke dakarun wanzar da zaman lafiya ciki har da sojoji daga Ruwanda don hana wani abu mai muni aukuwa. Su kadai ba za su iya tafiyar da wannan aiki saboda haka ana bukatar girke karin dakarun duniya a wannan kasa ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Baraka tsakanin Ruwanda da Faransa

Ruanda Genozid Gedenkfeier 07.04.2014 Zuschauer
Hoto: Reuters

Ita kuwa a labarinta game da jimamin kisan kiyashi a Ruwanda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta duba wata takaddama da ta kunno kai tsakanin Faransa da Ruwanda inda take cewa.

„Shekaru 20 bayan kisan kiyashi a Ruwanda baraka tsakanin gwamnati a Kigali da Paris ta sake yin girma, musamman game da rawar da Faransa ke takawa a Afirka. Faransa dai ba ta halarci bikin a Kigali ba a matsayin martani ga kalaman da shugaban Ruwanda Paul Kagame ya yi cewa Faransa na da hannu a kisan kiyashin, saboda dangantakarta da gwamnatin Hutun Ruwanda a wannan lokaci da suka yi wa 'yan Tutsi kisan kare dangi. Wannan ba shi ne karon farko da shugaba Kagame ya yi wadannan kalaman ba. A jawabin da ya yi shekaru 10 da suka wuce Kagame ya yi shagube ga tawagar Faransa da ta halarci bikin a birnin Kigali inda ya ce gasu zaune cikinmu amma ba su nemi gafara ba.“

Kwararowar bakin hauren zuwa Turai

An ceto mutane 4000 daga tekun Bahar Rum, sannan wasu dubbai a Libya suna shirin yin kaura, inji jaridar Der Tagesspiegel sannan sai ta ci gaba kamar haka.

Flüchtlinge in Lampedusa Italien Februar 2014
Hoto: picture-alliance/Ropi

„A cikin kwanaki biyu hukumomin Italiya sun ceto bakin haure 4000 daga tekun Bahar Rum, daukacinsu 'yan kasashen Eritrea, Ethiopia, Siriya da kuma yankunan Palasdinawa. Tun farkon wannan shekara ‘yan gudun hijira kimanin 15000 aka ceto a tekun Bahar Rum, kuma ba a san yawan wadanda za su yi kokarin bi ta wannan hanya mai hatsari don shigowa Turai ba. Rahotannin sun ce akwai ‘yan gudun hijira da bakin haure sama da 500000 a Libya da ke jiran daukar wannan kasada ta bi ta tekun Bahar Rum. A kowace shekara dubban ‘yan Afirka ke rasa rayukansu a tekun Bahar Rum a kokarin shigowa Turai.”

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe