1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damarmaki na zuba jari a kasashen Afirka

August 8, 2014

Taron hadin gwiwa na kwanaki uku da ya gudana tsakanin Amirka da kasashen Afirka a birnin Washington ya jaddada muhimmancin huldar cinikayya da zuba jari.

https://p.dw.com/p/1Crcr
USA-Afrika-Gipfel in Washington
Hoto: Reuters

A labarin da ta buga mai taken" Yanzu 'yan kasuwa masu zuba jari za su taka rawa a bunkasar tattalin arzikin Afrika" jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi: Yanzu har 'yan kasuwa Amurkawa na la'akari da matsayin Nahiyar Afirka. Ta ci gaba da cewar wajen shugabannin kasashe da gwamnatocin Afirka 50 ne suka samu goron gayyata daga wajen Obama zuwa birnin Washington, inda ya fara da yi musu alkawarin cewar kamfanonin Amirka za su zuba jari na dala biliyan 14 a wannan nahiya mai bunkasa a fannin kasuwanci. Tuni dai manyan kamfanoni kamar su coca cola da Hotel Marriot da Blackstone suka sanar da karin zuba jarin miliyoyin daloli a Afirka.

Ana iya cewar yanzu ne Amirka ta fara hangen abunda China ta jima da hangiowa a Afirka.

USA-Afrika-Gipfel in Washington
John Kerry da Idriss Deby na ChadiHoto: Reuters

Ana ganin cewar lokaci ne da suma 'yan kasuwan Jamus za su taka rawa a bunkasar tattalin arzikin na Afirka. Lokaci ya wuce da za'ayi wa nahiyar kallon mai fama da cututtuka da yake-yake da wasu bala'u.

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung cewa ta ke: da wannan taro na hadin gwiwa tsakanin Afirka da Amirka, ko shakka babu Washington ta hango irin alfanu dake wannan nahiya mai albarkatun kasa masu yawa. Wanda ba zai kasa nasaba da wannan yunkuri da ta yi kafin lokaci ya wuce mata ba.

Bullar cutar da ma irin barnar da ta yi kawo yanzu a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo dai ya kasance abun razanarwa, musamman bisa la'akari da cewar har yanzu tana ci gaba da yaduwa kuma babu alamun maganinta. Sai dai duk da wannan yanayi da ake ciki shugaban na Amirka ya tabbatarwa masu zuba jari cewar wannan matsala ce da za'a shawo kanta, kuma ba zata hana amfani da damarmarki da ke Afirka ba.

USA-Afrika-Gipfel in Washington
Salva Kiiir na Sudan ta KuduHoto: Reuters

A wannan makon ne mai shigar da kara a Afirka ta Kudu Gerrie Nel ya gabatar da jawabinsa karkare kararsa dangane da shari'ar zakaran tseren masaku Oscar Pistorius. A labarinta mai taken " zagayen karshe"Jaridar Süddeatsche Zeitung, tsokaci ta yi dangane da bayanan mai shigar da kara na dada tabbatar da cewar Oscar Pistorius ko shakka babu yana sane ya bindige budurwarsa Reeva Steenkamp, a cikin watan febrairun shekarata 2013. Duk da cewar ana zagaye na karshe na wannan fitaccen shari'a dake gudana a Pretoria, zai iya daukar wata guda nan gaba kafin a kammala shi.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal