1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakatar da tallafin da ake bawa Burundi

Ahmed SalisuMay 26, 2015

Kasashen da ke bawa Burundi tallafi sun fara janyewa saboda aniyar shugaban kasar ta yin tazarce, daidai lokacin da shugaban ke cewar ya na nan kan bakansa na yin tazarce din.

https://p.dw.com/p/1FWrw
Burundi Präsident Pierre Nkurunziza
Hoto: Getty Images/AFP/F.Guillot

Mahukuntan Burundi sun ce matsin lambar da suke samu daga kasashen ketare kan tazarcen shugaban kasar Pierre Nkurunziza ba zai sa ya jingine wannan aniya da ya dauka ba.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP matsayin gwamnatin ta shugaba Nkurunziza, inda ya ce har yanzu ya na nan ya na takara ta neman wani sabon wa'adi.

A hannu guda kuma gwamnatin ta Burundi ta bukaci al'ummar kasar da ke da kishin kasa da su bada tallafi na kudi don tallafawa hukumar zaben kasar wajen ganin ta gudanar da zaben shugaban kasa ba tare da ta fuskanci matsala ba.

Gwamnatin Burundin dai ta mika wannan bukata ce bayan da kasashen duniya suka fara dakatar da tallafin da su ke bata ciki kuwa har da wanda kungiyar tarayyar Turai ta EU ta ce za ta bayar don gudanar harkokin zabe kafin kasar ta shiga dambarwar siyasar da ta ke ciki a halin yanzu.