1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Chadi sun anso makamai daga Boko Haram bayan da suka yi nasara kansu

Abdulrazak Garba Baba-AniMarch 3, 2015

A karo na biyu daga karshen makon da ya gabata dakarun Chadi sun yi nasara kan Boko Haram, kuma sun kwato makamai da dama

https://p.dw.com/p/1EkVy
Tschad Armee Boko Haram
Hoto: Reuters/E. Braun

Rundunar sojojin kasar Chadi ta bada sanarwa cewar ta fatataki dakarun kungiyar Boko Haram a garin Dikwa da ke a yankin arewa maso gabashin tarrayar Najeriya inda ta ce ta kashe daruruwa daga cikinsu. Hafsan sojojin Chadi Ibrahim Sa'id ya rattaba hannu kan wata sanarwra da ke wa al'umma bayanin cewa a kokarin da Chadin ke yi na taimakawa makota wajen ganin bayan kungiyar nan ta Boko Haram, sojojin Chadi sun gwabza yaki da 'ya'yan kungiyar a garin Dikwa inda suka kashe daruruwansu, suka kuma kone musu babura da motoci da dama, hafsan sojin dai ya yi karin bayani kamar haka:

A bangaren dakarun Chadi da na kawayenta an yi hasarar mutun guda, a yayinda kimanin sojoji 34 suka sami raunuka masu tsanani. Hakan kuwa ya afku ne a yayin da motar nan da ke dauke da gangar iskar gas, ta tashi da wuta, wanda hakan ya yi sanadiyyar konewar sojojin 34.

Ko a karshen makon da ya gabata ma sojojin sun gwambza yaki da kungiyar a yankin tabkin Chadi inda suka kashe musu mutane kimanin 207 inda nan ma suka anshe musu motoci da babura har da babban tankin yaki da manya da kananan makamai.