1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola na yaduwa kamar wutar daji a Afirka

August 15, 2014

Cutar Ebola dake addabar Afirka a halin yanzu, ita ce ma tafi daukar hankalin jaridun Jamus a sharhunansu kan nahiyar ta Afirka a wannan mako.

https://p.dw.com/p/1CvLb
Liberia Westafrika Mann ließt Zeitung über Ebola
Hoto: Reuters

Jaridar Neue Zürcher Zeitung tace nahiyar Afrika tana fama da bala'i ne da ba'a hangi lokacin da zai kare ba. Cutar Ebola tana ci gaba da yaduwa kamar wutar daji, saboda duk matakan da aka dauka ya zuwa yanzu, sun kasa taimakawa a kokarin shawo kanta, ko akalla a rage yaduwarta. Jaridar tace hakan dai bai zama abin mamaki ba, domin kuwa da farko an kasa daukar hadarin wannan cuta da gaske, ga kuma batun al'adu da kin kula da tsoron da jama'a suke ji a kasashen da ta shafa. Jaridar Neue Zürcher Zeitung tace duk da haka, ma'aikatan jiyya da likitoci na cikin gida da likitocin kungiyar likitocin duniya dake kokarin rage yaduwar cutar a kasashe kamar Guinea da Liberiya ko Saliyo sun cancanci yabo da mai yawa.

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland tayi sharhinta ne a game da magungunan da kasashe da kungiyoyin duniya suke baiwa nahiyar ta Afirka domin yaki da Ebola. Wadannan magunguna, inji jaridar ya zuwa yanzu dai hukumar lafiyar ta duniya, wato WHO bata tabbatar da sahihancinsu ba, ganin cewar ya zuwa yanzu, kan dabbobi kadai aka gwadasu. To amma Amirka da kasar Kanada sun tura magungunan zuwa kasashen da cutar ta Ebola tafi yiwa illa, domin gwada su kan jama'a. To sai dai jaridar tace abin tsoro shine kada ayi fargar jaji, wato kada ya kasance wadannan magunguna sun zo ne a makare, ganin cewar ya zuwa yanzu, mutane fiye da 1000 ne suka mutu daga sakamakon kamuwa da wannan cuta a Liberiya da Saliyo da Guinea da kuma yan kalilan a Najeriya.

Jaridar Tagesspiegel a nata sharhin, ta duba halin da ake ciki ne a Libya da kuma yanayin zaman baki 'yan ci-rani, musamman yan kasashen Afrika bakar fata a can. Tace majiyoyi suna nuni da cewar kungiyoyi masu yaki da juna a kasar ta Libya suna amfani da 'yan ci rani na Afirka a matsayin sojojin tilas, inda musamman ta ambaci 'yan ci ranin da suka fito daga kasashen Eritriya da Habasha da Somaliya da 'yan Mali da Sudan, wadanda akan tilasta masu aikin bauta, misali jigilar makamai da sauran kayan yaki zuwa fagen daga. Kungiyar agaji ta kasar Italiya mai suna Habeshia tace 'yan Afirka da dama sun rasa rayukansu ta wannan hanya, wasu kuma sun sami rauni. Kungiyar tace al'amarin yafi muni a garin Misurata, inda 'yan Afirka akalla 700 mata da yara da maza majiya karfi daga Eritriya ake tsare dasu a matsayin bayi, har zuwa lokacin da za'a tura su fagen daga.

A karshe jaridar Tageszeitung ta duba Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ida tace daya daga cikin wakilan al'ummar musulmin kasar ne aka nada a matsayin sabon Pirayim minista, to sai dai Mahamat Kamoun da aka zaba, yana daya daga cikin wadanda suke da hannu dumu-dumu a aiyukan cin rashawa a kasar a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Michel Djotodia. Hakan ma ana iya cewar shine dalilin da ya sanya kungiyar musulmi ta Seleka tace ba zata amince dashi, ba kuma zai sami goyon bayanta kan wannan mukami ba. Ranar Lahadin da ta wuce shugaban kasa, Catherine Samba-Panza ta zabi Kamoun domin ya maye gurbin Andre Nzapaeke a matsyin Pirayim minista, tare da fatan zai sami nasarar shawo kan rikicin siyasa, musaman gaba dake tsakanin al'ummar musulmi da sauran jinsunan jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Nigeria Nnamdi Azikiwe International Airport in Abuja
Matakan tsaro saboda Ebola a NajeriyaHoto: Reuters

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar