1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola na jawo nakasu ga kasuwanci a Afirka

August 22, 2014

'Yan kasuwa da ke safara tsakanin Kamaru da Najeriya sun shiga wani hali bayan rufe kan iyakokin kasashen biyu sakamakon bullar cutar Ebola a tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1CzSn
Bildergalerie Virunga-Park Demokratische Republik Kongo
Hoto: WWF/Brent Stirton

Wannan batu na rufe kan iyaka dai ya sanya farashin kayayyakin ababan masarufi da ake shigar da su Kamaru daga Najeriya sun yi tashin gwauron zabi, domin kuwa kashi 80 cikin 100 na kayayyakin amfanin yau da kullum da ake shiga da su Kamaru na fitowa ne daga Najeriya.

Garin Idenaou da ke kudu maso yammacin Kamaru na daga cikin wuraren da wannan matsala ta shafa, wannan ya sanya rayuwar 'yan kasuwa musamman masu sayar da kayan lambu da ke shigarwa ko fitarwa da kaya cikin wani hali.

Lebensmittel im Überfluss in Uganda
Masu sayar da kayan gwari na daga cikin wanda rufe kan iyakar ya fi shafaHoto: DW/S. Schlindwein

Leba Yvette da ke garin na Idenaou ta ce mataki na mahukuntan Kamaru ya sanya rayuwar su cikin tsaka mai wuya, inda ta kara da cewar "na kan sayi ganyen Eru a Kamaru in kai garin Fatakwal a Najeriya don sayarwa. Da wannan sana'a ce na ke kula da rayuwata da ta 'ya'yana.''

Shi kuwa Rogers Bingwe wanda shi ma dan kasuwa ne cewa ya yi an sanya shi cikin wani hali don ya yi oda ta litattafai daga Najeriya amma ba za su shigo ba inda ya ce ga dalibai na shirin komawa makaranta kasa da makwanni biyu, wannan ne ma ya sa ya ce ''ina kira ga mahukunta kasar da su duba lamarin don a ceci fannin ilimi.''

Haka dai irin wannan matsala ke ci gaba da yin nakasu ga harkokin kasuwanci a bangarori daban-daban na kasar, inda a hannu guda yanzu lamarin ya fara shafar kasar Chadi da ita ma ke makotaka da Najeriya kana ta ke da iyaka da kasar ta Kamaru daga arewacinta.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Ahmed Salisu