1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola na ci gaba da daukar hankalin Jamusawa

Umaru AliyuSeptember 19, 2014

Jaridun na Jamus a wannan makoma sun sake maida hankalinsu kan cutar Ebola da ke addabar yankin Afirka Ta Yamma.

https://p.dw.com/p/1DFkp
Ebola in Liberia
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi tsokaci da taron kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a New York, inda majalisar ta yanke kudirin daukar mataki na duniya baki daya na yaki da wannan cuta. Jaridar ta ce a karon farko a tarihinsa, kwamitin sulhu yayi zama na musamman kan wata cutar da ta zama bala'i. Hakan ya bada damar nada wani kwamiti na gaggawa, wanda aka danka masa alhakin kai ziyara a kasashen da cutar ta Ebola tafi yiwa illa, domin ganin yadda za a shawo kanta. A zauren taron na kwamitin sulhu, Janar Sakatare Ban Ki Moon ya kwatanta Ebola a matsayin cutar da ta zama ta duniya baki daya, wadda tilas a hada kai domin shawo kanta.

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhinta ne kan cutar Ebola, inda ta tabo matakin da shugaba Barack Obama ya dauka na tura sojoji kimanin 3000 zuwa Afirka Ta Yamma, inda a can zasu taimaka game da gina wa kasashen da cutar ta shafa asibitoci da wuraren jiyya domin kula da marasa lafiya daga wannan cuta. Daga yanzu kuma zuwa wasu watanni shidda masu zuwa kuma, Amirkan za ta rika horad da ma'aikatan jiyya 500 ko wane mako a kasashen na Afirka ta yamma, kan hanyoyin kula da marasa lafiya da magunguna da yadda za su rika fadakar da iyalai game da rigakafin cutar.

Matsalar yunwa a duniya

Symbolbild Sierra Leone Hunger
Hoto: picture-alliance/dpa

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan mako ta yi magana ne kan rahoton hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya a game da matsayin masu fama da yunwa a duniya baki daya. Jaridar ta ce ko da shike an sami raguwar masu fama da bala'in yunwa a yanzu, sai dai nahiyar Afirka bata sami wani ci gaba ta wannan fuska ba. A yayin da batun kawar da yunwa yake daga cikin bukatun majalisar dinkin duniya karkashin shirin nan na muradun karni nan da shekara ta 2015, amma har yanzu ko wane mutum daya cikin mutane tara a duniya ke fama da matsalar yunwa. Ko da shike an sami ragi idan aka kwatanta da shekarun baya, amma al'amarin ba haka yake ba a Afirka, musamman a yankin nahiyar kudu da hamadar Sahara. A can din ba' sami raguwar masu fama da yunwa ba tsakanin shekaru 20 zuwa yanzu. A daura da haka ma, yawansu ya karu daga mutane miliyan 176 zuwa kimanin mutane miliyan 204. Hakan inji jaridar Neue Zürcher Zeitung yana nufin ko ane mutum daya cikin kutane hudu a Afika yana fama da matsalar yunwa kenan.

Kame 'yan ta'adda a Jamus da Kenya

Kämpfer von Al-Shabaab in Somalia
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F.-A.Warsameh

A karshe mujallar Der Spiegel ta sake maida hankalinta ga wasu Jamusawa da aka kama nan Jamus da Kenya, wadanda ake tuhumarsu da laifin kasancewa 'yan gwagwarmayar kungiyr tarzoma ta Al-Shabaab ta Somaliya. Jaridar ta ce irin abubuwan da suka fadi lokacin da ake masu tambayoyi, ya bada damar fara fahimtar wannan kungiya da yadda take tafiyar da ayukanta. Daya daga cikinsu ya ce ya shiga kungiyar ta Al-Shabaab ne saboda ya sami canji a rayuwarsa. Wani kuma yace ya shiga ne kawai domin ya ga yadda kungiyar take, sa'annan na uku da aka kama a nan Jamus yace ya shiga kungiyar Al-Shabaab ne domin ya koyi harshen yan Somaliya da al'adun kasar. Gaba daya Jamusawan da aka haifesu, suka kuma taso a nan Bonn, sun yarda da zargin cewar sun isa Kenya kafin su zarce zuwa Somaliya, inda suka hade da kungiyar Al-Shabaab, wadda ta horad dasu bisa dabarun aiyukan tarzoma.