1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar AIDS ko Sida—Rigakafi ya fi magani

January 29, 2009
https://p.dw.com/p/DrG7
Hoto: laif

Cutar AIDS ko Sida—Rigakafi ya fi magani.

Labarin da aka samu akan cutar da ke karya garkuwar jiki ko sida a nahiyar Afirka, na da daɗin ji in aka yi la’akari da cewa cutar ta ragu matuƙa musamman a ƙasashen da ta fi ƙamari, ko da yake duk da haka cutar ta fi yawa a nahiyar ta Afirka, saboda kashi saba’in cikin dari na masu ɗauke da cutar suna nahiyar Afirka.

Alƙalumman ƙididdiga na Majalissar Dinkin Duniya sun nuna cewa, aƙalla mutane miliyan biyu ne a Afirka ke kamuwa da cutar a kowace shekara.

Ƙasashen Afirka na iya ƙoƙarinsu na faɗakarwa akan illar cutar, amma da yawa suna jin cewa magana ce kawai domin ba su yadda akwai ta ba, waɗansu suna ganin suna da kariya da zaran sun yi wanka da ruwan zafi bayan sun sadu da mace.

Wani abu dake ciwa masu ɗauke da cutar tuwo a ƙwarya kuwa shine, ƙyama da ake nuna musu, shi ya sa da yawa masu ɗauke da cutar suke ɓuya. To amma a yanzu ana so a nuna wa masu ɗauke da cutar cewa ba ƙarshen rayuwa ba ce in kana ɗauke da ita, saboda da akwai magunguna da ake bayarwa kuma suna taimakawa wajen tsawaita rayuwar mai ɗauke da cutar muddin yana shan maganin.

Ji Ka Ƙaru

Burin da shirin Ji Ka Ƙaru ke so ya cimma shi ne, ya nunawa jama’a rashin fahimtar da ake da ita akan cutar da kuma yadda ake samun kariya daga kamuwa da cutar, za a kuma nuna yadda za ka zauna da mai ɗauke da cutar ba tare da mutum ya ɗauka ba.

An yi shirin na Ji ka Ƙaru a harsuna shidda, waɗanda suka haɗa da Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portuguese, da Amharic.

Shirin Ji Ka Ƙaru na samun gudunmuwa ne daga Ofishin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Jamus.