1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Afirka ta Tsakiya

July 24, 2014

Bangarori biyu da ke yaki da juna a kasar Afirka ta Tsakiya, sun rattaba hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta wanda ke da nufin kawo karshen fadan sama da shekara

https://p.dw.com/p/1CiVp
Versöhnungsforum in Brazzaville
Hoto: Pacome Pabandji/AFP/Getty Images

Sama da mutane miliyan guda ne dai suka tsere daga matsugunnensu domin neman mafaka, a yayin da dubbai suka yi asarar rayukansu, baya ga wadanda suka jikkata a wannan rikici da ya dauki sama da shekara guda yana gudana a Afirka ta Tsaki. A wannan Larabarce dai 'yan tawayen Seleka wanda musulmi ne, da abokan fadansu christoci watau Anti-Balaka, suka rattaba hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta a Brazzaville kasar Kongo. Kazalika wakilan gwamnatin Afirka ta Tsakiya da jam'iyyun siyasa da kungiyoyin ma'aikata da na al'umma da na addinai da shugaba Denis Sassou-Nguesso na Kongo, wanda ya shiga tsakani, duk sun sa hannu a yarjejeniyar.

David Smith, direkta ne a cibiyar tuntuba ta Okapi, kuma kwararre akan lamuran kasar ta Afirka ta Tsakiya.

" Fatan wannan tattaunwara ita ce, a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu. Kuma 'yan tawayen Seleke bayan kai ruwa rana, sun nuna kamar ba za su amince da sa hannu a yarjejeniyar ba, amma sai suka amince. Ko da yake rahotanni daga Brazzaville na nuni da cewar yarjejeniyar ta kunshi sharudda da yawa. Seleka ta bukaci a bata mukamai masu yawa a gwamnatin hadin kan kasa da za'a kafa a Janhuriyar Afrika ta Tsakiya".

Symbolbild Verbrechen gegen die Menschlichkeit Zentralafrika
Hoto: picture alliance/dpa

Har yanzu da ayar tambaya dagangane da ko akwai tursasawar da aka yi wa 'yan Selekan na amincewa da wannan yarjejeniya. Sai dai abunda ke da muhimmanci shi ne, an cimma wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta a wannan rikici na yankin Afirka ta Tsakiya. Duk da cewar a baya, yarjejeniya da Seleka bai cika tabbata ba.

Yarjejeniyar dai ta zo da mamaki, ganin cewar a wannan Litinin din ce shugaban Seleka Moussa Daffane ya bayyana cewar, sai an raba kasar tsakanin Arewaci da kudanci, kafin su amince da duk wata yarjejeniyar da za'a cimmawa. To shin darewar Afrika ta Tsakiyan biyu shine mafita a wannan rikici? Kwararre a akan lamuran kasar David Smith ya yi tsokaci

" A'a ko kadan, ina ganin furucin na Janar Moussa Daffane ba wani abu bane face sharan fage na neman karin madafan iko wa Seleka. Rahotanni daga Brazaville na nuni da cewar a yanzu haka Seleka ta ajiye wannan batu na raba kasar gida biyu, a wannan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma"

Symbolbild Verbrechen gegen die Menschlichkeit Zentralafrika
Hoto: picture-alliance/dpa

Sai dai dakarun kasashen Afrika na MISCA da na kasar Faransa da ake kira Sangaris da kuma MINUSCA na Majalisar Dinkin Duniya da ake shirin turawa Afirka ta Tsakiyar a watan Satumba, na da ra'ayin cewar dunkulalliyar kasa ce da ba za'a iya rabata ba.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Pinadao Abdu-Waba