1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisan Armeniyawa a Turkiya shekaru 100 da suka gabata

Lateefa Mustapha Ja'afarApril 24, 2015

Ministan harkokin kasashen ketare na Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce ba zai kira kisan Kiristoci Armeniyawa a Turkiya da kisan kare dangi ba.

https://p.dw.com/p/1FEeQ
Bikin tunawa da kisan Armeniyawa a shekara ta1915
Bikin tunawa da kisan Armeniyawa a shekara ta1915Hoto: picture-alliance/United Archives/TopFoto

Steinmeier ya bayyana hakane kwana guda bayan da shugaban kasar Jamus din Joachim Gauck ya bayyana kisan Armeniywan da daular Usmaniya ta yi a kasar Turkiya a shekara ta 1915 da kisan kare dangi. A yayin bikin tunawa da kisan Armeniyawan dai Shugaba Gauck ya yi tir da kisan, inda ya zamo shugaban kasar Jamus na farko da ya bayyana wannan kisa da na kare dangi. A hannu guda kuma ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta kasar Turkiya ta yi tir da bayyana kisan Kiristoci Armeniyawa da daular Usmaniya ta yi a shekara ta 1915 da kisan kare dangi da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi yayin da ya ke jawabi a wajen bikin cika shekaru 100 da kisan a kasar Armeniya.