1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China za ta kara kasafin ta na tsaro

Muntaqa AhiwaMarch 4, 2015

Kasar China za ta kara kudade ga fannin tsaron kasar ta a bana

https://p.dw.com/p/1EkfC
Myanmar Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa/Lynn Bo Bo

Kasar China za ta kara kashi 10 cikin dari a kasafin ta na bangaren tsaro, inda a yanzu kasafin zai kai dala biliyan 145 na Amirka.

Kamar dai yadda wani mai magana da yawun majalisar kasar Mr. Fu Ying ya tabbatar, kasar ta China za ta yi karin da aka ce da kadan ya zarta kasafin da aka yi a bara, na biyar kenan a jere da kasar ta ke kari kan kasafinta.

Mahukuntan Beijing dai sun alakanta karin kasafi ga tsaron kasar ne da samar da makaman kariya ga dakarun kasar da suka fi kowace kasa yawan mayaka.

Ana dai saran amincewa karin gobe Alhamis dama wasu kudaden da za a amincewa gwamnatin kasar wajen gudanar da harkokin kasa, kamar yadda mai magana da yawun majalisar Mr. Fu Ying ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Associated Press.