CDS Rahama na fuskantar barazanar rusawa
July 25, 2014
A cikin wata wasiƙa wacce ministan cikin gidan na ƙasar ta Nijar
malam Hasumi Masa'udu wanda shi ne ke kula da harakokin
jam'iyyun siyasa a ƙasar ya aike da ita ga shugaban jam'iyyar ya yi masa kashedi.
Gwamnati Nijar ta ce dole jam'iyyar CDS ta yi babban taronta na ƙasa
Ministan ya gargaɗi shugaban jam'iyyar Mahamane Ousmane da ya kira taron jam'iyyar da gaggawa domin sabinta manbobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar, ko kuma doka ta yi aikinta na soke jam'iyyar kwata-kwata. Wasiƙar gwamnatin dai ta ce ga ƙaida a cikin watanni shida ya zama wajibi jam'iyyar ta gudanar da taronta. Da yake mayar da martani wani jigo daga jam'iyyar ta CDS Alhaji Dudu Rahama cewa ya yi lokacin shirya taron nasu bai yi ba.
Yan tawaye na jam'iyyar sun ce za su kira taron ƙasa na jam'iyyar
Alhaji Abdu Labo mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa ya bayyana cewar cikin lokaci kaɗan za su gudanar da taron.
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto
Mawallafi : Gazal Abdu Tassawa
Edita : Abdourahamane Hassane