1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cadi ta ficce daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

April 4, 2014

Yayin da Tarayyar Turai ta sanar da batun zuwan dakarunta kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kasar Cadi kuwa tayi shelar janye nata dakarun.

https://p.dw.com/p/1BcIA
Tschad Militär
Hoto: JEAN LIOU/AFP/Getty Images

Al'umma a birnin Bangui na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da sanarwar da kasar Cadi ta yi na janye dakaru daga wannan kasa, inda akasarin al'ummar wannan birni, ke nuna farin cikin a bayyane kan wannan mataki na kasar Cadi, duk kuwa da cewa hukumomin na Bangui sun nuna bakin ciki kan wannan mataki ganin cewa kasar ta Cadi tana da karfin fada aji a yankin Afirka ta tsakiya.

Zargi kan dakarun kasar Cadi

Dakarun kasar Cadi dai sun kasance cikin tsaka mai wuya, tun bayan da aka zarge su da laifin bude wuta ga fararan hula ba tare da wata tsokala ba.

A wannan Jumma'ar ma dai kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun jadda zargin da ake yi wa dakarun na Cadi, inda suka ce sun kashe mutane a kala talatin a makon da ya gabata, kuma an shafe dukkanin wannan sati ana cece-kuce kan wannan batu, yayin da kowa ke fadar ta bakin sa.

Shi ma dai mai magana da yawun hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakin Bil-Adama Rupert Colville, ya zargi dakarun kasar ta Cadi da laifin buda wuta ga fararan hullar, yayin daga nashi bengare Sakatare Janar na MDD Ban Ki-Moon, yayi Allah wadai da gallazawa fararan hula da ake yi a wannan kasa.

Tschad Militär Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa

Saidai tuni masu lura da al'ammuran yau da kullun ke ganin cewa, janyewar dakarun kasar Cadi, duk da cewa akwai batun isowar dakarun Tarayyar Turai na EUFOR, babban koma baya ne ga matakan dawo da zaman lafiya a wannan kasa, kamar yadda Micheal Loutouboue, kwararre a ofishin bincike da yada labarai kan batun zaman lafiya da tsaro dake kasar Belgium yayi bayani....

"Dakarun kasa da kasa dake Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a halin yanzu basu wadatar ba,domin ya kyautu ace an kai ga soja dubu goma zuwa dubu 12, kafin a fara tsammanin shayo kan matsalar, dan haka janyewar dakarun kasar Cadi duk kuwa da an sanar cewa dakarun Tarayyar Turai na EUFOR zasu iso, zata kawo babban cikas a kokarin da ake na gama kasar da dakaru."

Da yake magana kan wannan batu a wannan Juma'a, Ministan harkokin wajan kasar ta Cadi Moussa Faki Mahamat, yace matakin dakasar sa ta dauka na janye dakarunta, ba gudu ba ja da baya, tunda kowane zargi kansu yake fadawa.

Tunanin dawo da Chadi kan bakanta

Sai dai Micheal Loutouboue, kwararre a ofishin bincike da yada labarai kan batun zaman lafiya da tsaro dake kasar Belgium, da ya saurari sanarwar kasar ta Cadi kan batun janye dakarun nata, na ganin cewa akwai yuyuwar a tantamna, har ma a shayo kan Cadi ta dawo kan maganarta yana cewa....

Zentralafrikanische Republik Ausschreitungen Gewalt Christen Muslime 16.01.14
Hoto: picture-alliance/AP

"Lalle ban san abun da Allah zaiyi ba, amma, kun ji cikin sanarwar da Cadi ta fitar,tace zata tantamna matakan janyewar ta da hukumomi na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kuma kasar Cadi na cikin wannan kungiya ta kasashen Afirka ta Tsakiya, sannan kuma ta kasance mai mahimmanci ga ayukan kiyaye zaman lafiya a wannan kasa, ni a ganina, akwai wuya ace zasu kai ga janye dukkan dakarun su, ina ganin za'a ci gaba da tataunawa dan shayo kan kasar ta Cadi, domin kasashen biyu suna da babbar dangantaka, dan haka kasar Cadi na daga cikin hanyoyin walwale matsalar rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya."

Daga nata bengare kungiyar kare hakin Bil-Adama ta Amnesty Internationale, tace janyewar dakarun kasar Cadi ba wai yana nufin cewa sunci bulis kan zargin da ake musu na taka hakin Bil-Adama a wannan kasa ba.

Amma kuma duk da haka ana ganin cewa da wuya ne dakarun Tarayyar Turai na EUFOR, su kai ga cike gibin da ake da shi na bukatun soja a wannan kasa bayan ficewar dakarun kasar ta Cadi.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba