1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata su ne ginshikin ci gaban kowacce al'umma

Al-Amin Sulaiman MuhammadMarch 6, 2015

Ranar takwas ga watan Maris na kowacce shekara rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin bikin ranar mata ta duniya da nufin yin nazari akan bunƙasa ci gabansu.

https://p.dw.com/p/1EmtV
matan da kungiyar Boko Haramta tilastawa barin gidajensu
matan da kungiyar Boko Haramta tilastawa barin gidajensuHoto: Reuters

Taken bikin na bana dai shi ne “Ƙarfafa mata shi ne ƙarfafa ɗan Adam” da ma halittu baki ɗaya. Ƙasashen da suka ci gaba dai kan mayar da hankali wajen ƙarfafa mata a matsayinsu na masu rauni a cikin al'umma inda ake ba su dama kwatankwacin yadda ake bai wa maza a kusan dukkanin fannoni na rayuwa. Hakan a cewar masana da masu gwagwarmayar kare hakkokin mata ya taimaka gayya wajen kyautatuwar al'amura tare da bunƙasar rayuwa a irin waɗannan nan wurare.

Latifa Nabizada, matukiyar jirgin sama a Afghanistan
Latifa Nabizada, matukiyar jirgin sama a AfghanistanHoto: S. Marai/AFP/Getty Images

Mace ita ce ginshikin rayuwar al'umma

Ko me ake nufi da ƙarfafa mata wanda ke zama ƙarfafa bani Adama ko kuma ma halitta baki ɗaya a cewar Uwar gida Grace Mcdonald Garba shugabar wata ƙungiya ce mai ƙarfafa matasa wato Teenagers Empowerment Initiative a turance idan aka ƙarfafa mace to tabbas tana da damar da za ta ƙarfafa gidanta da 'ya'yanta da 'yan uwanta har ma da sauran al'umma baki ɗaya. A wannan shashi na duniya musamman Tarayyar Najeriya ƙalilan daga cikin mata ne ke samun tallafi da nufin ƙarfafa su a fannonin ilimi da na tattalin arzikin ƙasa inda aka bar wa wasu ƙungiyoyi hakkin karfafa mata.

Ƙalubale ga rayuwar mata

Duk da cewar akwai wasu gwamnatoci da ke fito da shirye-shiryen da nufin ƙarfafa mata ta hanyar koya musu sana'oi da ba su basussuka don fadada kasuwancin su sai dai ba kasafai shirye-shiryen kan dore ba saboda dalilai na siyasa da harkokin mulki. Wannan a cewar masu fafutukar kare hakkin mata na zama ƙalubale a kokarin fitar da matan daga kangin da suke ciki na kuncin al'adu da suka mayar da su baya tsakanin al'umma. Rashin samun tallafi da kuma baiwa mata dama shi ne ake dangantawa da rashin samun nasara a ƙokarin da matan ke yi na samun mukamai na siyasa ko kuma lashe zaɓuka musamman idan suna yin takara da maza. Masu iya Magana dai na yi wa mata kirari da cewa “in baku babu gida”.

Matan kasar Ghana a gona suna aiki
Matan kasar Ghana a gona suna aikiHoto: Geoffrey Buta