1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar agazawa tsofaffin 'yan tawaye

Salissou BoukariOctober 9, 2014

Hukumar kare hakin dan Adam ta Human Rights Watch, ta zargi gwamnatin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango da yin rikon sakainar kashi ga tsofaffin mayakan kasar.

https://p.dw.com/p/1DS64
Hoto: picture alliance/dpa

Fiye da mutun dari daga cikin tsofaffin mayakan kasar da aka kwancewa damara da iyallansu ne suka rasa rayukansu sakamakon yunwa da kuma rashin lafiya a wani barakin soja na Kotakoli bayan da masu kula da su suka ki basu abinci tare da kula da lafiyar su. Wannan matsala da kungiyar kare hakin dan Adam ta Human Rights Watch din tayi tsokaci a kanta dai ta faru ne a wani yanki na Arewa mai nisa maso yammacin kasar ta Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwangon, inda fiye da tsofin 'yan tawaye 1000 tare da iyallansu ke zama. Wannan dai ba shi ne karon farko da aka samu wannan matsala ba tunda aka fara tsarin nan da aka kira DDR, na kwance damararsu tare da samar musu ayyukan yi na fuskantar matsaloli na karancin kayan aiki da sauran ababen bukata.

Kokarin kungiyoyi masu zaman kansu

Elisere Ebayya shi ne sakataren wata kungiya mai zaman kanta a yankin Arewacin gundumar Oubangui inda aka fuskanci wannan matsala ga abin da ya ke cewa...

" Mu munyi namu kokari har ma sai da mukayi aiki tare da hukumomin kiwon lafiya na wannan gunduma da ma shugaban asibitocin yankin Gomeba Mbengo dan ganin yadda zamu iya taimakawa wadannan mutane, to amma har yanzu maganin wannan matsala na hannun gwamnatin Kongo."

A karshen shekara ta 2013 ma yayin wani rangadi na gani da ido a garin Borebana dake nisan a kalla kilomita 50 da birnin Goma a gabashin wannan kasa, shaidun gani da ido sun ga yadda ake tafka kura-kurai a kan yadda ya kamata a kula da tsofaffin 'yan tawayen da suka ajiye makamansu inda hakan ya sanya wasunsu ke kai hari ga al'umma yayin da wasu ma ke komawa ga aikinsu na tawaye, abun daya kasance wani babban kalubane ga babban zaman taron kasa da kasa na kasashen dake kewaye da manyan tabakuna ko yankin grand Lac.

Gwamnati na neman tallafin kasashen duniya

Boduin Amoli shi ne shugaban wannan tsari a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango ya kuma ce....

"Lalle mun yi farin ciki da goyon bayan da rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Kongo ta MONUSCO ke bayar wa, da ma na sauran kungiyoyin kasa da kasa, amma ina ganin kan wannan tsari na tsofaffin 'yan tawaye da sauran 'yan gudun hijira dole sai da taimakon kasashen duniya."

Halin kunci da tsofaffin mayakan na kasar Kwango ke ciki a halin yanzu na zama wani babban kalubale wajan cimma burin da aka sanya a gaba cikin wannan tsari na kawo karshen tawaye ta hanyar kwance damarar mayaka.