1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rantsuwar kama mulki a Tarayyar Najeriya

Ubale Musa/LMJMay 29, 2015

Sabon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi ragamar mulkin Tarayyar Najereiya inda zai kwashe tsawon shekaru hudu a kan karagar mulkin.

https://p.dw.com/p/1FZ2B
Rantsuwar kama mulkin sabon shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari
Rantsuwar kama mulkin sabon shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Reuters/A. Sotunde

Cikin yanayin tsananin tsaro da halin dar-dar ne shugabanni da ma wakilai daga sassa daban- daban na duniya da suka hada da sakataren harkokin waje na kasar Amirka John Kerry da kusan dukkanin shugabannin yankin yammacin Afirka dama takwarorinsu irin Jacob Zuma na Afirka ta Kudu da Robert Mugabe na Zimbabuwe suka bi sahun al'ummar kasar wajen bikin mai dinbin tarihi da daukar hankali. An dai buga fareti a bangaren sojoji, an kuma yi Owambe na mawaka duk dai da nufin murnar ranar da ta kama hanyar sake dora kasar bisa sabuwar alkibla ta siyasa da tattali na arziki.

Hare-haren ta'addanci a Najeriya
Hare-haren ta'addanci a NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo/A. Adamu

Rashin tsaro da dinbin fata

Duk da cewar dai bikin na bana bai kai na shekarun can baya ba bisa hujjar rashin tsaro da halin alhinin da kasar take ciki, ranar ta zamo ta murna ga 'yan kasar da a cewar Buharin suka manta da banbancin da ke a tsakaninsu wajen rungumar ta zuwa tudun muntsira. To sai dai kuma sabon shugaban da ya karbi mulki a cikin dogon fata dama buri a bangaren al'umma na kasa, bai yi wata-wata ba wajen nuni alkibla ta gwamnatinsa a yanzu dama a nan gaba. Da farkon fari dai ya ce yana shirin tunkarar matsalar Boko Haram kai a tsaye, dama dauke shelkwatar tsaron kasar ta Najeriya zuwa birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno har sai an samu nasara.

Gadon tarin matsaloli

Ko bayan batun rashin tsaron da ya dauki lokaci mai tsawo, a jawabin nasa na tsahon mintuna 20 dai Buharin da ke da shekaru 72 a duniya da kuma ke da jan aikin sauyi na akala ga kasar da ke cikin wani yanayi, ya tabo matsalar tattalin arzikin kasar da ya ce na cikin halin ni 'yasu dama rashin wutar da yace ya zamo abun kunya a daukacin kasar a halin yanzu. Tun kafin kare bikin dai shugaban da ya bar gadon dama mataimakinsa suka fice daga zauren na "Eagles Square" suka kuma kama hanyarsu zuwa garuruwan Otuoke da na Kaduna da ke zaman mahaifa a garesu. Abun kuma da ya bude sabon babi na shugabanci a kasar da ke yiwa kanta kirari na giwa ta Afirka amma kuma ta dauki lokaci tana tangal-tangal.

Shugaban Najeriya mai barin gado Jonathan tare da sabon shugabanta Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya mai barin gado Jonathan tare da sabon shugabanta Muhammadu BuhariHoto: Reuters/Afolabi Sotunde