1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bouteflika ya sake lashe zaben Aljeriya

April 18, 2014

Shugaban kasar Aljeriya mai ci yanzu Abdelaizi Bouteflika ya samu kashi 81,53% na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa da ya gudana ranar Alhamis.

https://p.dw.com/p/1Bku6
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Sakamakon farko na zaben shugaban kasar da ya gudana a kasar Algeriya, ya bayyana Abdelaziz Bouteflika, a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 81,53% na kuri'un da aka kada. Abokin hamayyar sa Ali Benfils ya zo a matsaiy na biyu inda ya samu kashi 12,18%. Sai kuma Abdelaziz Belaïd da ya samu kashi 3,36%. Snnan Louisa Hanoune ta samu kashi 1,3%.

An kiyasta adadin wadanda suka fito suka yi zaben a matsayin kashi 51,7% na wadanda suka yi rejista, duk kuwa da kiran da 'yan adawan kasar suka yi na a kauracewa zaben. Da ma dai tun kafin zaben, ake ikirarin cewa Shugaba Bouteflika ne zai lashe zaben, a gaban yan adawar kasar da ke da rabuwar kawuna. Da farko dai dan takara Ali Benfils, yayi watsi da sakamakon inda ya ce an tafka babban magudi a cikinsa.

Shugaba Bouteflika dai dan shekaru 77 da haihuwa, ya kwashe a kalla shekaru 15 a kan karagar mulkin kasar ta Aljeriya, inda a halin yanzu ya samu wani sabon wa'adi na hudu. Sai dai kuma sakamakon na wannan lokaci, bai kai ga na shekarar 2009 inda ya samu kashi 90% na kuri'un da aka kada.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe