1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta dauki hankalin jaridun Jamus

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 6, 2015

Yaki da Boko Haram a Najeriya da makwabtanta da yaki da 'yan tawayen FDLR a Kwango da yaki da Ebola na daga cikin batutuwan da suka dauki hankali jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1EmcR
Goodluck Jonathan im Boko Haram Gebiet Baga
Hoto: picture-alliance/dpa

Bari mu fara da sharhin da die Tageszeitung ta yi a kan yaki da Boko Haram a tarayyar Najeriya da kuma makwabtanta. Jaridar ta ce ba ranar da Allah zai wayi gari ba tare da rundunar sojojin Najeriya ta ce ta samu nasara a kan kungiyar Boko Haram ba. Sai dai kuma wannan ci gaban mai hakon rijiya ne, saboda a daidai lokacin da ta kwato gari daya daga hannun wannan kungiya da ke da tsaurin ra'ayin addinin, Boko Haram din na sake kai hari a wani gari na daban a arewacin Najeriyar. Wannan kuma a cewar die Tageszeitung ba ya rasa nasaba da tsunduma kanta har iya wuya da rundunar da sojojin Najeriya ta yi cikin harkokin siyasa. Ita ce dai ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin cewar an dage zaben shugaban kasa daga 14 ga watan Fabreru zuwa 28 ga watan Maris bisa dalilai da ta danganta da na tsaro.

Jaridar da kara da cewa da kamar wuya rundunar sojojin Najeriya ta murkushe wannan kungiya kafin zaben 28 ga watan Maris ganin yadda cin hanci da kuma rashin tarbiyar sojoji suka yi katutu. Sai dai kuma shiga yaki gadan-gadan da kasashen kamaru da Chadi da Nijar suka yi ya sa Najeriya canza kamun ludayinta a ynukurin ganin bayan Boko Haram, inda a karon farko kungiyar da kanta ta yarda cewar mayakanta da dama sun rasa rayukansu a fito na fito da sojojin taron dangi.

'Yan Najeriya na gudun hijira a Kamaru
'Yan Najeriya na gudun hijira a KamaruHoto: AFP/Getty Images/R. Kaze

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta mayar da hankali ne kan yaki da cutar Ebola da ake yi a yankin yammacin Afirka cikin wani sharhinta mai taken har yanzu ba a rabu da Bukar ba.Ta ce yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola a yankin yammacin Afirka a makon da ya gabata bai taka kara ya karya ba. Amma kuma bai kamata a manta cewa rayukan mutane kusan dubu wannan cuta ta lamshe a tsukin shekara guda ba a kasashen Gini da Laberiya da kuma Saliyo.

Guinea na ci gaba da yaki da Ebola
Guinea na ci gaba da yaki da EbolaHoto: DRK

Saboda ganin a shawo kan wannan cuta kwata-kwata ne ma, Kungiyar Gamayyar Turai da kuma kasashen da Ebota ta fi addaba da kuma wakilan kasashen 70 na duniya suka gudanar da taro a birnin Brussels. Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce hanya daya da za a bi wajen kawar da cutar Ebola ita ce hada karfi da karfe tsakanin gwamnatin wadannan kasashe da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, ta hanyar gina ingantattun asibitoci tare da samar da kwararrun likitoci da kuma kayan aiki.

Bari mu karkare da tsokacin da Die Tageszeitung ta yi a kan yaki da sojojin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango ke yi da 'yan tawayen FDLR, inda ta ce suna samun nasara. Jaridar ta ce tun shekaru 20 da suka gabata ne Kungiyar tawaye ta FDLR ta ke cin karenta babu babbaka a gabashin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango. Baya ga kisan babu gayra da dalili da kungiyar ta yi kaurin suna a kai, ta mayar fyade mata tamkar wani abin ado.

Kwango ta kama 'yan FDLR da dama
Hoto: Simone Schlindwein

Jaridar ta ce tun ranar Alhamis ne sojojin na kwango suka kwato sansanoni biyu daga hannu 'yan tawayen. Sannan kuma suna ci gaba da kai farmaki da nufin ganin bayan 'yan tawayen da ke neman zama gagarabadau. Babban abin da suka sa a gaba shi ne kama shugaban mayakan FDLR Sylvestre Mudacumura, wanda kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ke nema ruwa a jallo.