1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar Jamhuriya karo na 56 a Nijar

Gazali Abdu Tasawa daga YamaiDecember 18, 2014

Babbar kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasar wato ANDDH ta zargi gwamnati da 'yan siyasar da karan tsaye a dimokradiya adaidai lokacin da kasar ke tunawa da ranar Jamhuriya.

https://p.dw.com/p/1E73f
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

Kungiyar ta ANDDH ta bayyan wannan matsayi nata ne a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta nuna rashin amincewarta da yanda gwamnatin kasar ke tunkarar wasu koke-koke na wasu kungiyoyin kwadago na kasar.

Kungiyar ta ANDDH ta fitar da wanann sanarwa tata ne biyo bayan wani zama da ta gudanar inda ta yi bitar tafiyar al'amura da dama na kasar dauka tun daga na siyasa zuwa na zamantakewar alumma. Da ya daga cikin batutuwan da kungiyar ta ANDDH ta ambato a cikin sanarwar tata shine abun da ta kira sakin layin da gwamnati da wasu yan siyasa ke yi a cikin tafiyar da harakokin siyasar kasar musamman a fannin hulda tsakanin jam'iyyun ko kuma tsakanin 'ya'yan jamiyya daya.


To saidai yanzu haka wasu kungiyoyin na ganin kungiyar ta ANDDH ba ta tunkari matsalar ta hanyar da ta dace ba .Malam Abdu Lokoko na kungiyar ROSEN na ganin gwamnati ba ta da laifi a cikin wanann lamari matsala ce ta 'yan siyasa da shari'a ce ke maganinta.

Niger Tende Festival in Zinder
Hoto: DW/L. Mallam Hami



Haka zalika kungiyar ta ANDDH ta gargadi gwamnatin Niger da ta gaggauta shawo kan matsalar yajin aikin da kwararrun likitoci ke ta fama yi akan neman hakkokinsu domin kawo karshen wahalhalun da marasa lafiya ke gani yau watanni da dama a sabilin yaje-yajen aikin kungiyar kwararrun likitocin kasar ta Nijar ta SMES sanann kuma ta bukaci gwamnatin da ta dauki matakin karbar 'yan Nijar da aka fara korowa daga kasar Aljeriya ta yanda za su koma garuruwansu a cikin mutunci.