1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayani kan kwayar cutar Ebola

August 6, 2014

Ita da cutar Ebola cuta ce da akan dauke daga jiin dabbobi irin su birrai da jamegu da makamantansu. Cutar dai na daga cikin irin cutakan da kan yi saurin hallaka mutane.

https://p.dw.com/p/1CpDS
Ebola Ausbruch in Uganda
Kwayar cutar EbolaHoto: picture-alliance/dpa

Likitoci sun ce alamun kamuwa da cutar sun hada da zazzabi mai zafin gaske da amai da gudawa mai jini da kuma fidda jini ta kafofin jikin da suka hada da dubura da mafitsara da kunne da hanci da baki.

Daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar sun hada da cudanya da wanda ke dauke da cutar ta yanda alal misali mutum zai hadu da yawun mai cutar ko gumi ko wani nau'i na ruwa. Kazalika jami'a da mai dauke da cutar na iya jawo Ebola.

Hanyoyin da za bi wajen kare kai daga kamuwa daga cutar Ebola sun hada da kaurace wa cin naman biri ko jemage ko kuma da sauran naman daji da ake wa lakabi da ''Bush Meat''. Har wa yau likitoci sun ce za a iya kaurace wa kamuwa da cutar ta hanyar nisantar mai ita da kiyaye tsafta ta jiki da muhalli da yawaita wanke hannu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal