1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban kamen fararen hula a Nijar

Abdoulaye Mamane AmadouMay 25, 2015

Jami’an tsaro masu farin kaya sun cabke dan gwagwarmayar kungiyoyin fararen hula Nuhu Arzika tare da tuhumarsa da yi wa tsaron kasar zagon kasa.

https://p.dw.com/p/1FWEp
Moussa Tchangari, Journalist und Menschenrechtler
Hoto: DW/ Thomas Mösch

An tsawaita wa'adin kamun da yan sanda ke yiwa Moussa Tchangari sakamakon alaka da Boko Haram, a yayin da yan sanda na farin kaya PJ suka cabke fitaccen dan gwagwarmayar nan Nuhu Arzika da zarginsa da yiwa tsaron kasa zagon kasa

A Jamhuriyar Nijar a yayin da hukumomi a kasar na kara tsawaita wa'adin binciken da jami'an tsaro ke yi wa fitaccen dan gwagwarmayar nan na kungiyoyin fararen hular Alternative Moussa Tchangari, da wasu kwanaki biyar masu zuwa bayan cika kwanaki na ka'ida n afarko.

A hannu guda kuma jami'an tsaro na 'yan sanda masu farin kaya ne suka cabke wani dan gwagwarmayar kungiyoyin fararen hula Nuhu Arzika tare da tuhumarsa da yi wa tsaron kasar zagon kasa. Tsawon kwanaki uku dai ne hukumomin 'yan sandan suka yi suna gudanar da bincike akansa, kana daga bisani suka cabke shi a wannan Lahadin.

Kawo yanzu dai babu wani ko wata hukuma da ta bayyana zargin a hukumance sai dai lauyoyinsa sun tabbatar da ci gaba da gwagwarmaya face sai sun ga sun kubutar da shi.