1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages
Wrong language? Change it here. DW.DE has chosen Hausa as your language setting.
  • Die Kommissionschefin der Afrikanischen Union (AU), Nkosazana Dlamini-Zuma bei einem Gipfel der AU in Addis Abeba am 16.07.2012. (c) dpa - Bildfunk+++
pixel

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Mace da kamar maza a AU

    A 2012 aka zabi Nkosazana Dlamini-Zuma a matsayin mace ta farko da za ta shugabanci hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayyar Afirka. Tsofuwar ministar cikin gidan Afirka ta Kudu ta rungumi wani sabon salon shugabanci, a cewar wadanda suka shaidar da kwanaki 100 na kamun ludayinta. Amma kuma ta na da jan aiki a gabanta wajen ciyar da mambobi 53 gaba tare da magance rikice rikice da suke fama da su.

  • OAU- Gipfel im Mai 1963 in Addis Abeba (/AFP/Getty Images)

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Hadin kai maimakon rarrabuwar kawuna

    A Lokacin da aka kafa Kungiyar Hadin kan Afirka (OAU) a ranar 25 ga mayun 1963, kasashe 30 da suka riga suka samu 'yancin kansu ne suka zama membobinta. Burin da shugabannin wancan lokaci suka sa a gaba shi ne cetota daga rugujewa. A wannan lokaci ana fama da yakin cacar baka, kana ana samun sabanin ra'ayi game da mulkin mallaka da ke ci. Wannan hoton na taron OAU na shekarar 1966 ne.

  • Der Äthiopische Kaise Haile Selassie mit Ghana Präsident Kwame Nkrumah (L) während der Gründung der OAU, STR/AFP/Getty Images

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    'Yan rajin Afirka daya al'uma daya

    Kwame Nkrumah (a hagu), shugaban farko na kasar Ghana da takwaran aikinsa Haile Selassie na Ethiopiya (a tsakiya), sun yi ruwa da tsaki wajen kafa OAU. Nkrumah ya yi begen ganin nahiyar ta zama "Hadeddiyar nahiyar Afirka" domin ta samu karfin kalubalantar kasashen yamma da suka ci gaba, tare da bunkasa tattalin arzikinta. Sai dai haryanzu kasashen da suka samu 'yancin kai ba su bayar da kai ba.

  • Ein Banner bei einer Demonstration von schwarzen Studenten in Soweto, Südafrika, auf dem steht Der Kampf geht weiter (AP Photo)

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Hada karfi domin yakar Apartheid

    Babbar manufa da Kungiyar Hadin kan Afirka ta sa a gaba a shekaru 10 na farko shi ne yaki da Apartheid wato wariyar launin fata a kasar Afitka ta Kudu.Da ma tun a shekarunta na farko wato a shekarun 1970 OAU ta hada karfi da karfe, inda ta kafa kwimiti da ke goyon bayan gaggwarmaya da makamai da 'yan kasar ke yi domin yakar Apartheid.

  • Eine Hacke im Einsatz auf einem afrikanischen Feld.
DW/ Peter Hille

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Sabon tsari na tattalin arziki

    OAU ta kafa wani tsari a shekarar 1980 a Lagos da nufin bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka. Wannan yarjejeniya ta tanadi yin tsudeni in tsudeka a sigar cinikayya tsakanin kasashen Afirka kafin shekara ta 2000. Sai dai har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba. A shekarar 1991 ma an sake cimma wata sabuwar yarjejeniya a Abuja da ke neman cika wannan buri a Afirka kan nan da shekara ta 2025.

  • Westsaharische Frauen in einem Flüchtlingscamp (c) dpa - Bildfunk+++

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Akidar kawo karshen mamaya

    Duk da ka'idar da ta gindaya na kin shata wata sabuwar taswira a Afirka, amma kuma a 1982 OAU ta amince da "Jamhuriyar larabawa ta Sahraouie"l a matsayin 'yantaciyar kasa bayan da Polisario ta ayyanata. Saboda haka ne Moroko ta raba gari da kungiyar. Ya zuwa yanzu dai ita ce kawai ta fita daga kungiyar ta kasashen Afirka tun bayan kafata..

  • Ugandas Präsident Yoweri Museveni bei seiner ersten Kabinettssitzung 1986 OFF/AFP/Getty Images

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Sukar manufar tarayya

    Rikicin Sahara Moroko na ci gaba da zama halin ba sabon ba na OAU. Ta ci gaba da amfani da manufarta ta rashin yin shisshigi. Ko da a yakin basasa a Rwanda ma, ta yi ta sara ta na duban bakin gatari.Saboda haka ne wasu 'yan boko ke danganta taron kolinta na Addis Abeba da taron 'yan kama karya. Daya daga cikin masu wannan ra'ayi, shi ne Yoweri Museveni da ya dare kan kujerar mulkin Uganda a 1986.

  • Burundische Soldaten bei der Beerdigung des Präsidenten Melchior Ndadaye, der bei einem Putsch 1993 ums Leben kam ALEXANDER JOE/AFP/Getty Images

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Kin amincewa da juyin mulki

    A farkon shekarun 1990 OAU ta canja kamun ludayinta game da rikice rikicen da ke kunno kai a kasashen Afirka. Saboda haka ne ta kafa wani tsari na wanzar da zaman lafiya a cikinsu.Ko da a lokacin da sojoji suka gudanar da juyin mulki a Burundi a 1996, sai da ta aza wa kasar takunkumi. Sai dai ba ta cika amfani da wannan tsari ba saboda matsaloli ciki har da na kudi da OAU ta ke fama da shi.

  • Südafrikas Flagge zwischen anderen Fahnen der AU-Mitgliedsländer im Hauptquartier in Addis Abeba Xinhua /Landov

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Sannu ba ta hana zuwa

    Kasaitacen biki OAU ta shirya lokacin da Afirka ta Kudu ta zama mamba a 1994, shekaru 30 bayan kafata.Tun daga wannan lokaci kasar ta Afirka ta Kudu ta ke ta taka muhimmiyar rawa a cibiyar OAU da ke birnin Addis Abeba, kasancewarta daya daga cikin giwayen nahiyar.

  • Gaddafi bei einem AU-Gipfel 2006.

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Girka sabon babi a OAU

    Bayan karshen yakin cacar baka da kuma na Apartheid a Afirka ta Kudu OAU ta fara neman dora kanta akan wata sabuwar turba a 1999. Shugaban Libya Muammar al-Gaddafi (anan lokacin taron 2006) ya bayar da shawarar farfado da shirin kafa "Hadeddiyar nahiyar Afirka". Ya yi amfani da dukiyarsa wajen ganin cewa haka ta cimma ruwa.

  • Zulu Tänzer bei der Gründungszeremie der AU in Durban, Südafrika 2002 ALEXANDER JOE/AFP/Getty Images

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Daga OAU zuwa AU

    Hakar Gaddafi ba ta cimma ruwaq ba. Maimakon haka ma rarrabuwar kawuna aka samu tsakanin kasashen Afirka bayan rikidewar kungiyar OAU zuwa Kungiyar Tarayyar Afirka AU a birnin Durban na Afirka ta Kudu a shekara ta 2002.Yarjejeniyar kafa AU ta bai wa kasashe membobinta damar ci gaba da cin gashin kansu.

  • Nelson Mandela überreicht ein Bild mit einem Emblem des Panafrikanischen Parlaments im Jahr 2006 FATI MOALUSI/AFP/Getty Images

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Tafiyar hawainiya na hukumomi

    AU ta dauki Kungiyar Tarayyar Turai a matsayin abin misali wajen cimma burin da ta sa a gaba, na kafa majalisar dokokin kasashen Afirka. A 2004 ta yi nasarar kafa wannan majalisa a karon farko da ta kunshi mambobi 235 da suka fito daga kasashe 47. Sai dai ratar da ke tsakanin majalisar da kuma cibiyar Au da ke birnin Addis Abeba na nunawa a fili zahirin yadda al'amura ke tafiyar hawainiya.

  • AU-Soldaten in Darfur . (AP Photo/Jose Cendon)

    Jerin ayyukan AU cikin shekaru 50

    Sabon tsarin zaman lafiya

    A farkon shekarun 2000 rikice rikice sun shafi kashi 20 cikin 100 na 'al'umar nahiyar Afirka walau kai tsaye ko kuma a fakaice. Samar da dawwamammiyar zaman lafiya na ci gaba da zama burin AU. A 2004 ta kafa kwamitin zaman lafiya da tsaro da ke da hurumin kai dauki idan rikici ya barke a wata kasar Afirka. A wannan shekarar ce Au ta tura da sojoji domin kare fararen hula a Darfur na Sudan.


    Mawallafi: Maja Braun | Edita: Mouhamadou Awal/ SUS

SHIRYE-SHIRYE

Rediyon DW koyaushe a cikin kunne

Kuna iya sauraron shirye-shiryen DW a harsunan Afirka guda shida kai tsaye (hausa, swahili, amharik, ingilishi, faransanci, harshen Portugal) a duk lokutan da aka saba. Idan sun wuce ku, kuna iya sauraren shirye-shiryen Hausa ta „Audio on demand“! Kuna iya zaben abin da za ku saurara daga jerin shafunan dake ƙasa.

Kuna iya tuntuɓarmu akan wannan adireshi: hausa@dw.de ko kuma ku aiko mana da gajeren saƙo akan wayarmu mai lamba: +49-173-7100428.