Siyasa da zamantakewa na da muhimmanci wajen samar da irin sauyin da ake muradi na inganta ci gaban al'umma.
Kula da lafiya abu ne dake da tasiri a rayuwa. Kamar yadda akan ce lafiya jari, kasancewar ita ce Uwar jiki, domin sai da ita ake komai. Babu babban arziki da yafi samun ƙoshin lafiya.
Shirin Radiyon Deutsche Welle na ilimantarwa wa nahiyar Afirka. Waɗanda Suka kunshi wasannin kwaikwayo da bayanai akan siyasa, Kiwon lafiya, Tattali da dai sauran su!
Kashi na ɗaya:
Laraba 13:30 UTC, Juma'a 18:30 UTC da Asabar 18:05 UTC
Kashi na biyu:
Juma'a 13:30 UTC, Asabar 13:20 UTC da Litinin 18:40 UTC
Duniya na cigaba da fuskantar sauyin yanayi. Wane tanadi muke da dashi na kalubalantar wannan juyi da Duniya take ci? Kamar yadda kuma yake da muhimmanci mu samu hanyar bunkasa tattalin arziki domin dogaro ga kai.
Zaman lafiya da juna, su ne ginshiƙin ci gaban ko wace Al'umma. Ta haka ne za'a daraja wa juna tare da samar da haɗin kan aiki tare domin samar da ingantacciyar ci gaba da Al'uma ke muradi.
Muna farin ciki tare da marhabin da ra'ayoyin masu sauraro, dangane da shirinmu na Ji Ka Karu. Kuna iya aiko mana ta adireshimmu na Email ko kuma ta Wasika.
Shirin Ji Ka Ƙaru sai daɗa bunƙasa yake yi! An samu ƙarin ƙwararru masu sha'awar shirin da suka haɗe da mu domin ƙara kyautata shirin saboda jin daɗin masu sauraro. Ga dai fuskokin sabbin masu taimaka wa shirin Ji Ka Ƙa