1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar barkewar yakin basasa a Ukraine

April 16, 2014

A wata ganawar wayar tarho da ya yi da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi gargadi kan matakin soji da Kiev ta dauka.

https://p.dw.com/p/1BjYX
Internationales Wirtschaftsforum in St. Petersburg Merkel und Putin
Hoto: DW/A. Brenner

Furucin na Putin na zuwa ne bayan da hukumomin Ukraine suka aike da tankunan yaki zuwa yankin gabashin kasar da ke da 'yan aware magoya bayan Moscow.

Rahotanni daga birnin Slaviansk na kasar Ukraine na nuni da cewar, tankunan yaki dauke da jami'an soji guda shida sun shiga wannan gari da ke yankin gabashin kasar.A cewar wadanda suka gane wa idanunsu dai, dukkan motocin na dauke da turar Rasha. Motocin dai sun tsaya a kofar ginin majalisar birnin na Slaviansk, inda 'yan aware da ke goyon bayan Rasha suka jima da mamaye shi.

Wannan zuwa ne bayana tattaunwar wayar tarho da ta gudana tsakanin shugaba Vladimir Putin da shugabar gwamnatin Jamus Angelan Merkel. Shugabannin biyu dai sun jaddada muhimmancin tattaunawar bangarori hudu da aka tsara yi a wannan Alhamis a birnin Geneva tsakanin jami'an diplomasiyyar Rasha da Tararrayr Turai da Amurka kana da Ukraine.

EU Außenministertreffen Krim Referendum 17.03.2014 Ashton
Catherine AshtonHoto: Reuters

Amfani da matakin diplomasiyya

Jami'an diplomasiyyan dai na cigaba da kira ga Rasha data janye dakarunta da suke zargin na jibge a kan iyakar Ukraine, kamar yadda kantomar kula da harkoki ketare ta Kungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton ta nunar;

" Ya zamanto wajibi a tsayar da wannan yunkuri na kawo tashin hankali a Ukraine. Muna goyon bayan kare 'yancin, mutunci da hadin kan al'ummar Ukraine. Akan haka ne muke kira ga Rasha da ita ma ta mutunta wannan, tare da janye dakarunta daga kan iyakar Ukraine".

Sojojin Ukraine din dai sun karfafa madafan ikonsu a garin Kramatorsk da ke ta gabashi, bayan sun sanar da kwace filin saukar jiragen saman garin da ke hannun yan aware da suka mamaye gine-ginen gwamnati. Manyan tankunan yaki guda bakwai dauke da tutocin Ukraine din ne suka yi amfani da karfi akan, mutanen da suka kira 'yan bindiga dake da goyon Moscow.

Wannan sabon yunkuri na amfani da kafi wajen karbe madafun ikon gabashin Ukraine din dai, na zuwa ne a jajibirin tattaunawar bangarorin hudu a wani sabon mataki na gano bakin zaren warware rikicin na Ukraine, matakin da ya dace bangarorin biyu su yi la'akari da shi, a cewar sakatare harkokin wajen Britaniya Willam Hague.

Ya ce" wannan kyakkyawar dama ce wa Rasha na nunar da cewar a shirye take, na yin amfani da diplomasiyya wajen warware wannan rikicin".

Shugaba Putin ya fadawa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewar, wannan mataki da gwamnatin Ukraine ta dauka na amfani da matakan soja akan 'yan aware ya sabawa tsarin mulki. A cewarsa dai wannan zai iya jefa kasar yakin basasa. A hirasa da manema labaru a Vietnam kafin ya shige zuwa birnin Geneva a gobe, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce kamata yayi Kiev ta saurari al'ummarta da kunnen basiri, ba da karfin soji ba.

EU Außenminister Treffen 04.04.2014 in Athen Steinmeier mit Hague
Ministocin harkokin waje na EUHoto: DW/B. Riegert

Yiwuwar kakaba karin takunkumi a kan Rasha

Kasashen yammaci na Turai din dai a ta bakin ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ba zata ji nauyin karawa Rashan takunkumi idan ta ci gaba da abun da ya kira "kauce wa hanya".

" Za mu gudanar da taron shugabannin kasashe da gwamnatoci domin kakabawa Rasha karin takunkumi, a mako mai zuwa idan hakan ta kama. Manufar Faransa da Nahiyar Turai zai ci gaba da kasancewa tursasawa Rasha, idan har matakai na diplomasiyya basu warware matsalarba".

Yanzu haka dai kallo ya koma kan yankin gabashin kasar ta Ukraine, inda ake kokarin yin fito na fito tsakanin sojojin Kiev da 'yan aware da ke goyon bayan Rasha, a jajibirin tattaunawar diplomasiyya kan wannan rikici.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu