1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira sun rasu a gabar ruwan Italiya

Ahmed SalisuApril 19, 2015

Mutane akalla dari bakwai ne aka bada labarin hallakarsu lokacin da suke kokarin ketara teku don shiga nahiyar Turai daga Afrika.

https://p.dw.com/p/1FAkp
Italien Migranten
Hoto: picture-alliance/dpa/Italian Navy Press Office

Masu gadin na gabar ruwan Italiya suka ce mutanen wandanda bakin haure ne na makare cikin wani kankanin jirgin ruwa wanda ya nutse da su gabannin isarsu tsibirin nan na Lampedusa.

Wani mutun da ya tsira da ransa ya ce jirgin ya kife ne lokacin da mutanen da ke cikinsa suka jirga zuwa bangare guda na jirgin daidai lokacin da wani jirgi da suke zaton zai cece su ya nufo kusa da su.

Wannan dai shi ne karo na biyu a 'yan kwanakin da suka gabata da aka samu hadari makamancin wannan. Hakan ne ma ya sanya kantomar harkokin wajen ta kungiyar EU Federica Mogherini ta ce ministocin harkokin waje na kungiyar ta EU za su tattauna don samo hanyoyin magance faruwar hakan.