1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Badakalar cinikin jarirai a Nijar ta dauki sabon salo

Yusuf BalaNovember 28, 2014

A yayin da kotu ta ba da belin wasu daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a cinikin jarirai tsakanin Nijar da Najeriya, har yanzu tsugune bata kare ba.

https://p.dw.com/p/1DwD1
Südniger junges Mädchen mit ihrer Mutter
Hoto: DW/N. Conrad

Wannan badakalar ta kai ga yin gudun hijira tsohon shugaban majalisar dokokin Nijar Hama Amadou wanda mai dakinsa ke daga cikin wadanda ake zargi kuma har yanzu tana hannun hukumomin kasar ta Nijar. Yanzu haka dai an zabi Amadou Salifou a matsayin sabon shugaban majalisar dokokin kasar.