1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bada ilimi ta amfani da fasahar zamani

Abdulrahman Kabir/ASMay 20, 2015

Kasashen Afirka sun bi sahun takwarorinsu na Turai da sauran nahiyoyi wajen amfani da fasahar zamani don bada ilimi a matakai daban-daban ko da dai a kan fuskanci kalubale.

https://p.dw.com/p/1FTEN
Eröffnung des E-Learning-Zentrums in Balbala, Dschibuti
Hoto: SOS-Kinderdörfer weltweit

Sannu a hankali wannan tsari na bada ilimi ta hanyar amfani da fasaha ta zamani da aka fi sani da e-learning na shiga sassa daban-daban na tarayyar Najeriya. Makarantu masu bada ilimi mai zurfi da kuma kungiyoyi da suka nakalci tsarin ne ke amfani da wannan dama don ilimantar da al'umma.

To sai dai fa duk da cewar an kawo kan wannan gaba, masana na ganin cewar akwai tazarar gaske tsakanin yadda lamarin ya ke a Najeriya da sauran sassan duniya domin kuwa akwai karanci na maida hankalin hukumomi wajen samun nasarar shirin da ma kayan da za a yi amfani da su. Wata matsala har wa yau da aka bankado ita ce rashin cikakken ilimi na amfani da na'ura mai kwakwalwa.

Yayin da masana ke kokawa kan matsalolin da suke ganin za su zama tarnaki wajen amafana da wannan shirin, su kuwa daliban da gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tura makarantu daban-daban don samun ilimi na ganin abin ba haka ya ke ba kuma a cewarsu tsarin na baiwa mutum dama wajen yin harkokinsa na karatu ba tare da fuskantar kalubale ba, kana sun ce ko matsalar rashin yawan na'urar kwamfiyuta da aka ce ana da ita ba lallai ta kasance koma baya ga tsarin ba don dalibi zai iya samu a cibiyoyin da ake karantawar ta irin wannan tsari na e-learning.

E-Learning-Zentrum vom VDR in Dschibuti eröffnet
Kasashen Afirka da dama sun rungumi wannan tsari na e-learning da ake gani mai sauki wajen samar da ilimiHoto: Christof Alexander Schwaner_VDR

A daura da wannan muhawarar da ake yi, wasu na ganin duk da cewar kasashenmu na Afirka na cikin rashi na ingantaccen tsari na koyarwar da na'urar kwamfiyuta, nan gaba lamarin zai sauya duba da yadda ake cigaba da rungumarsa kuma wasu na ganin amfani da ake yi da wayoyin hannu irin na komai da ruwanka din nan zai taimaka wajen fadada wannan tsari ta yadda mutanen da dama za su amfana.