1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba wa hammata iska a majalisar Kenya

Ahmed SalisuDecember 18, 2014

A ranar Alhamis dinan (18.12.2014) majalisar dokokin kasar Kenya ta yi zaman kan dokar yaki da ta'addanci , sai dai yayin zaman masu adawa da dokar sun tada hatsaniya.

https://p.dw.com/p/1E71G
Kenia Parlament Austritt Römisches Statut
Hoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Hayaniya da ma doke-doke gami da keta takardun wasu mambobin majalisar da ke dauke kunshin wannan kudurin doka ne dai suka mamaye zaman majalisar da safiyar yau, dalilin da ya sanya kakakin majalisar dage zaman zuwa wani dan lokaci don maido da doka da oda a gidan.

kungiyoyin kare hakkin bani adama na ganin dokar fa wata hanya ce ta yin karen tsaye ga hakkin bani adama duba da irin abubuwan da ta kunsa. Kazalika su ma 'yan jarida sun koka dangane da kunshin dokar wanda a cewarsu hakan zai hana su rawar gaban hantsi. Yusuf Lule shi ne shugaban hukumar kare hakkin dan Adam na kasar ta Kenya ya kuma shaidawa DW irin matsayinsu kan wannan batu:

Parlamentsabstimmung Kenia Nairobi Wahlen Parlament
Hoto: AP

"Mu 'yan kungiyar fararen hula mun damu matuka game da kunshin wannan kuduri domin zai yi kafar ungulu ga irin fafutukar da muka yi ta samun 'yanci. Kudurin dokar zai tauye hakkin wanda ake zargi da laifi wajen shari'a sannan zai bawa soja damar tsoma baki a wuraren da ya kamata a ce fararen hula ne ke iko da su ko ma tatsar bayanai na mutane ko da kuwa ba su amince ba".

To sai dai duk da irin tutsun da 'yan adawa da ma kungiyoyin al'umma suka yi dangane da bijiro da wannan doka da za ta baiwa gwamnati tatsar bayanai da girka hukuma ta musamman da za ta dakile harkoki na ta'addanci, a gefe guda Dr. Charles Oteino da ke zaman kwararre kan gyare-gyare na tafiyar da mulki da kuma hukumomi masu zaman kansu na ganin yunkurin ya dace ko da dai ya aza ayar tambaya kan wasu batutuwa:

Kenianisches Parlament debattiert über neues Sicherheitsgesetz - Polizei
Hoto: AFP/Getty Images/S. Maina

"Samar da hukumar yaki da ta'adancin abu ne da ya dace to amma ayar tamabaya da za mu aza ita ce karkashin wacce hukuma za ta kasance, kazalika za ta zama mai cikakken iko ne ko kuma za ta zamto karkashin ikon rundunar 'yansandan kasar"