1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta yi kira da hada karfi wajen yakar Boko Haram

Salissou BoukariJanuary 30, 2015

Shugabar kwamitin Tarayyar Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma ce, ta sanar a wannan Jumma'a cewa kungiyar Boko Haram ta kasance wata annoba ga zaman lafiyar kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/1ETRP
Hoto: picture alliance/dpa/Gcis

Shugabar ta yi wadannan kalammai ne ya yin zaman taron kungiyar da ke gudana a halin yanzu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Babban zaman taron kungiyar da zai gudana a ranakun Jumma'a da kuma Asabar, ya zabi Shugaban kasar zimbabwe Robert Mugabe dan shekaru kusan 91 da haihuwa, a matsayin sabon Shugban kungiyar Tarayyar Afirka wanda ya canji Shugaba Ould Abdul Aziz na kasar Mauritaniya a wannan shugabanci na karba-karba.

Batun kashe-kashen al'umma da kungiyar ta Boko Haram ke ci gaba da yi ne dai ya dauki hankalin wannan taro, inda kwamitin Sulhu da zaman lafiya na kungiyar, ya yi kira da a kafa wata runduna mai dakaru 7.500 domin fuskantar kungiyar ta Boko Haram wadda kawo yanzu ta yi sanadiyya mutuwar mutane fiye da 13.000. :