1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU na shirin taimaka wa Najeriya yakar Boko haram

Ludger Schadomsky/ Pinado Abdu-WabaJanuary 28, 2015

Kungiyar Tarayyar Afirka na tattauna batutuwa da dama a taronta na koli ciki har da kashe-kashen da Boko Haram ke yi a Arewa maso gabashin Najeriya, da rikicin Sudan ta Kudu da kuma tasirin annobar Ebola a Afirka.

https://p.dw.com/p/1ESMM
Hoto: Getty Images

Abin da aka riga aka tantance daga cikin zantattukar kawo yanzu dai shi ne kungiyar AU za ta yi wata ajiyar kudade na musamman don yaki da ayyukan ta'addanci a Afirka. Za kuma ta ba da kudurin samar da runduna ta musamman, amma ba a kai ga fayyace inda rundunar za ta sami kudaden shiga da ma irin suffar da za ta dauka ba.

Sai kuma sakatariyar zartaswar Kungiyar gamayyar Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma ta ce lokacin daukar matakin bai daya dan kashe wutar wannan matsalar da ke cigaba da ruruwa a Najeriya ya yi. Ta ce "Mun firgita kwarai da irin abin tausayin da Boko Haram ke cig aba da janyowa mutanenmu, sace 'yan mata, kone gidajen mutane, firgita al'ummomi da kisa. Da farko karamar kungiya ce ,yanzu muna ganin yadda take fadada zuwa yankin yammacin Afirka da tsakiyar Afirka. ."

Dr Nkosanzana Dlamini Zuma
Dr Nkosanzana Dlamini Zuma ta AU na so a yaki Boko KaramHoto: DW/G. Tedla

Matakin soje da Kungiyar AU za ta dauka kan Boko Haram tare da kudaden da ya kamata su ware dai, shugabanin kasashen Afirkan sun tattauna akai tun watan Satumban shekara ta 2014 a Nairobi. Kuma a wannan taron na Addis Ababa za su amince da tura rundunar da ta kunshi dakaru kusan dubu uku zuwa kasashen da abin ya shafa, Najeriya, Nijar, Benin, Chadi da Kamaru.

Har yanzu dai ba a kai ga girka rundunar ko ta kwanan da aka yi wa lakabi da Africa Stand by Force ba. Sai dai kuma AU ta ce za ta sake girka wata rundunar ko ta kwanan, wadda aka kira African Capacity for Immediate Response to Crisis a turance. Babu wata alama cewa za a cimma wannan buri kamar yadda Judith Vorrath daga wata gidauniyar kimiyya da siyasa da ke Berlin, wadda ke bincike kan zaman lafiya da tsaro a Afirka ta bayyana

"A ce wai ana neman girka wata cibiya wadda ba a tantance yadda zata saje da sauran cibiyoyin ba, ana neman wata hanya ce ta samun mafita cikin gaggawa, ba tare da la'akari da yiwuwarsa ba, bayan kuma ba za a iya tantance hi bisa la'akari da tsarin zaman lafiya da tsaro cikin sauki ba. Yanzu dai bisa dukkan alamu suna bukatar mafita cikin gaggawa"

Kamerun Mora Armee Soldaten Anti Boko Haram 07/2014
Sojojin kamaru na samun taimakon takwarorinsu na Chadi a yaki da Boko haramHoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Dangane da Sudan Ta Kudu kuma, ba a bayyana ko kunguiyar ta AU za ta iya bayyana karfin ikonta ba, ko ma za a wallafa rahoton binciken da aka yi kan yadda ake take hakkin bil Adama a kasar ba. A tsakiyar watan Janairu ne wakilin sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan kare hakkin bil Adama ya nuna cewa akwai wadansu munanan abubuwa wadanda shugaba Salva Kiir zai so ya boye.