1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

APC: "Ya kamata kwararru su binciki kudin yaki da Boko Haram"

Ubale Musa daga AbujaNovember 13, 2014

Jam'iyyar adawar ta ce labarin kanzon kurege ne shugaban Najeriya yake fadi cewa ya yi nisa a kokarin kai kasar tudun na tsira.

https://p.dw.com/p/1DmSW
Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

A wani taron manema labaran da ta kira da ranar Alhamis dinnan (13.11.2014) a Abuja fadar gwamnatin Najeriya jam'iyyar ta APC ta ce kasar tana fuskantar barazana mafi girma a cikin tarihin ta na shekaru hamsin da kadan sakamakon rashin iya mulkin jam'iyyar PDP da take ci yanzu haka.

Ga dai karuwa ta cin hanci a fadar jam'iyyar , ga kuma rashin tsaron da ya yi kanta, sannan kuma ga rashin sanin makama ta shugabanci a bangaren masu mulkin kasar da ke ci yanzu duk dai a fadar APC, da ta yi nazari sannan da mai da martani ga kalaman shugaban kasar na sake kaddamar da takarar sa a wannan mako.

Alhaji Mai Mala Gubio dai na zaman sakataren jami'yyar APC na kasa, kuma a fadarsa rashin tausayi dama sanin shugabanci ne ga Jonathan din na kaddamar da takarar tasa a dai dai lokacin da jini ke kara malala ta ko'ina a kasar.

"In ka duba yanzu arewa maso gabas kullum jinin jama'a ake zubarwa da asarar dukiya, ba karatu ba noma, kuma a wannan hali ne shugaban kasa ya kaddamar da kansa a daidai lokaci da ake jana'izar yara a Potiskum. Wannan ya nuna halin ko in kula saboda in ka duba kasashen da suka cigaba zaka ga in ana jimami to dakatar da komai ake ko da kuwa rai daya aka rasa”

Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Janar Buhari me ritaya da Atiku Abubakar 'yan takarar shugabancin Najeriya a APCHoto: Atiku Media Office

APC da ta kai ga ambato dalla dalla na irin badakalar cin hanci da ma rashin mutunta hakkin 'yan kasar da ke zaman ruwan dare a bangaren masu mulkin kasar ta Najeriya, a halin yanzu dai ta ce alamar rashin sanin banbancin dama cikin hagu ne dai ya sanya daya a cikin wadanda suke fuskantar shari'ar kwashe kudin kasar da suna na tallafin man fetur ne kuma ke jagorantar kokarin sake dawowa da shugaban kasar kan gadon mulki, kan batun matsalar tsaron da ke neman wucewa da sanin kowa a kasar dai jam'iyyyar ta kuma nemi kaddamar da bincike na kasa da kasa kan yadda gwamnatin Tarrayar Najeriya ke tafi da yakin ta'ddancin kasar a halin yanzu abun kuma da a cewarta ke nuna alamar da biyu.